Yadda zaman kotu ya kasance da abduljabbar Nasiru kabara.
Lauyan dayake wakiltar gwamnatin jihar Kano barista Sa’ida ya bukaci kotu tasa a binciki kwakwalwar Malan Abduljabbar Nasiru Kabara a asbiti.
Dogaro da sashi na dari biyu da saba’in da takwas cikin baka da shari’a na jihar Kano. Barista Sa’ida ya nemi hakan ne a lokacin da ake tsaka da saurarar Shari’ar Malan Abduljabbar Nasiru Kabara.
An saurari Shari’ar a wata babbar kotun shari’a musulunci da ke Kofar Kudu, karkashin mai shari’a sarki Yola.
Wakilin Hausa Daily News Ibrahim Babangida ya bayyana mana cewa, Dalilin dayasa lauyan Barista Sa’ida ya bukaci hakan. Yace hakan ya biyo bayan karantawa Abduljabbar Nasiru Kabara lefin da ake tuhumarsa dashi har guda Hudu.
Amma ko da aka tambayeshi akan tuhumar bece komai ba ko ya aikata laifin ko bai aikata ba Anan ne malamin yayi shiru ya kasacewa komai.
HaKan yasa baristan ya bukaci kotu ta kai malamin asibiti domin duba kwakwalwarsa.
Mungode da ziyartar shafinmu