Advertising
Advertising
Uncategory

Alamu sun nuna cewa ruwa yay tsami tsakanin Jarumin kannywood Naburiska da Afakallah

Ruwa yay tsami tsakanin Mutapha Naburika da Shugaban tace fina finai hausa Isma’il Na’abba Afakallah.

Advertising

Mustapha Naburiska da fitaccen Darakta Sunusi Oska 442 sun bayyana dalilansu na fita daga gurin taron hadin gwiwar tsakanin masana’antar fina finan hausa da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nigeria wato (NDLEA).

Taron anyishi ne don tatauna yadda za’a kawo matsalar shareshaye daya addabi matasan jihar kano.

Taron anyishi ne kakashi kungiya masu tace fina finai wato (WOPPAN) Tare da hadin kai da hukumar sha da fataucin miyagu kwayoyi (NDLEA).

Advertising

Taron an gudanar dashi a ranar 1 ga Satumba 2021 wajen taro dake gidan talabijin din kannywood.

Wakilin mu ya shaida mana cewa fitar Mustapha Naburika da Darakta Sunusi Oska daga dakin taron an dangantata da shigowar isma’il Na’abba Afakallah.

Darakta Sunusi Oska da Mustapha Naburiska dawasu ragowar yan film sunyi shigar fararan kaya irinta jam’iyar hamayya ta kwankwasiya.

Darakta da sauran yan film din da sukai faraf shiga sun sami wajen zama daya daga chan baya suna tataunawa kafin a fara gabatar da taron.

Da isowar Afakallah sai Mustapha Naburiska da Sunnusi Oska da sauran masu farafen kayan duk suka fita daga gurin taron hakan yasa aka danganta fitar tasu da Shigowar Afakallah.

Wannan abu daya faru yaja ce ce ku ce a masana’antar bayan faruwar hakan Hausa Daily News ta kira Jarumi Naburiska dan jin abinda yasa suka fita inda yace bahaka ne yasa suka fitaba.

Haka shima daracta Sunusi Oska 442 ya musallata zagin da yan masana’antar keyi na sun fita ne sabida Afakallah ya shigo ne suka fita.

Ku kasance da shafinmu dan samun ingantatun labarai.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button