Advertising
Advertising
Labarai

Zamu saukaka farashin kayan abinci-Gwamnatin Kano

Gwamnatin jahar kano na yin kurin saukaka farashin kayan masarufi na amfanin yau da gobe.

Advertising

Hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano, ta bayyana shirin ta na saukaka farashin kayan abinci a fadin jihar kano.

Shugaban hukumar Mahmoud Balarabe ya bayyana haka ne a wata ziyara da manema labarai suka kai masa a ranar Alhamis din da ta gabata.

A cewar shugaban hukumar ta damu da yadda kayan abinci suka tashi a hannun Manyan ‘yan kasuwa wanda hakan ya na wahalar da talakawan jihar kano.

Advertising

Shugaban hukumar ya ce ba za su zuba ido ana irin wannan zalincin ba suna kallon mugayen ‘yan kasuwa suna dora wa al’uma wahala ba, Ya kara da cewa duda wahalar da al’uma ke Nigeria.

Hausa Daily News ta ji ra’ayoyin jama’a inda da yawan su suke cewa ba wannan ne karo na farko da hukumar tace zata saukaka farashin kayan masarufi ba.

Shugaban Hukumar yace yanzu muna aiki akan korafe kofen jama’a ne da majalisar jihar kano dan ganin Gwamnatin tasa dokar tursasa yan kasu su saukaka kayan abinci.

Shugaban yace Ba za mu zura ido muna ganin mutane suna yin yadda suka ga dama ba.

Shugaban ya bayyana shirin su na ganin sunyi tarbiya yara ta hanyar koya musu sana’a tun daga makaranta dan ganin yaran sun taso da abinyi su ba tare da sun dogara dana wasu ba.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button