Da Dumi Dumi: Gwamnatin tarayya na yin kurin saka dogar yin allurar rigakafin corona ga duk ma’aikata
Gwamnatin Nigeria Na shirin daukar kwakwaran maraki akan mutanan da suke kin yadda ai musu allurar riga kafin ciwon corona akasar.
Ranar talatar data gabata ne Shugaban Hukumar kula da cibiyoyin lafiya na hukumar kiwon lafiya na kasa Faisal Shu’aib ‘NPHCD’ yayi wata sanarwa a wani taron manema labarai a abuja.
KARANTA KUMA: Abin tausayi: Wani yaro ya bayyana yadda yake ji idan yasha tabar wiwi
Shugaban yace gwamnati zatabi tsarin doka wajen tilas tawa mutane da suka ki yadda da ayi musu allurar riga kafin korona domin a dakile yaduwar cutar a kasar.
Ranar Alhamis din data gabata shima saka taren gwamnatin Boss Mustapha yace gwamnati zata tilasata yin allurar ga duk wani ma’aikacin gwamnatin tarayya.
KARANTA KUMA: Matashi yayi ikirarin bazai sakkoba matuka bai mashi aure ba
Boss Mustapha ya kara da cewa zuwa yanzu gwamnatin an samu yiwa mutin sama da kimanin biliyan uku kuma daga cikin su mutun miliyan daya sunyi allurar zagaye na biyu.
Idan zaku iya tunawa makon daya gabata ne wata babbar kotun fatakwal da ke Jihar Ribas ta dakatar da gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo daga hana mutane shiga coci-coci da Masallaci sai da katin allurar rigakafin corona.