Labaran Kannywood

Jarumin kannywood Mustapha Naburiska yayi amai ya lashe a wata hira dayayi

Fitaccen Jarumi a masana’antar Shirya fina finai ta kannywood Mustapha Naburiska yayi Amai ya lashe a wata hira da gidan Radio Freedom kano tayi dashi.

Jarumin kannywood yace ya cire jar hular ya rubgumi tafiyar Gwamna Baba Ganduje kadumul islam.

Fitaccen jarumin kannywood Mustapha Naburaska ya ce, ya cire jar hula ya rungumi tafiyar Gwamna Umar Ganduje.

KARAN TA KUMA: Alamu sun nuna cewa ruwa yay tsami tsakanin Jarumin kannywood Naburiska da Afakallah

Kaman yadda kuka sani dai jarumin ya dade yana tafiyar jamiya (PDP) cikin kungiyar kwankwasiya, Hakan yasa aketa ganin kamar bazai iya barin tafiyar jar hula.

Ya fadi hakan ne a wata zantawa da gidan da Freedom Radio tayi dashi a daren Asabar. ya ce ya cire jarhula domin ba gadar sa akayi da ita ba.

Naburaska ya kara da cewa da hakoransa 32 aka ganshi, don haka duk wanda zai taimaki sana’arsu shi yake so yake kauna.

KARANTA KUMA: The issue of Zahra Diamond and Mustapha Naburiska marriage

Jarumin yace a duk Najeriya in ka cire garin Legas babu inda Gwamna yake tsan tsar aiki kaman gwamnatin kano a dalilin haka ya dawo tafiyar Baba Ganduje.

Bayan wannan hira da gidan Radio sukai dashi jarumin ya dora wani bayani a shafin sa na Instagram inda ya musa abin da ya fada kaman yadda zaku gani a kasan wannan rubutu.

Shafin Mustapha Naburiska

Na buriska ya wallafa hotonsa Mai sanye da jar hula a shafinsa na Instagram yana mai cewa sana’a ta daban siyasa ta daban, Dan haka duk Wanda yace zai taimaki sana’ata Nima zan taimaki tashi, Dan haka har yanzu ina tafiyar kwankwasiya.

Mungode da ziyarar Hausa daily News.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button