Da Dumi Dumi: Nasiru Sarkin waka ya saka makudan kudade ga wanda ya gano masa wasu mutane- Labarin Hausa
Shararen mawakin hausa wanda aka dade ana damawa dashi wato Nasiru sarkin waka ya saka wasu makudan kudade ga duk wanda ya gano masa wasu mutane.
Nasiru sarkin waka yayi rantsuwa yace wllh duk wanda aka samu yana daya daga cikin wanda suke daukar wakar sa suna turawa manyan mutane da suan su sa bazai basu ba.
Kalli Bidiyo kashedin naziru Sarkin waka anan kasa.
Jarumin ya wallafa wani bidiyon sa a shafinsa cikin fushi, Yana mai cewa:
Zanyi magana ne akan wasu bata gari da suke cutar da masoya na, Kuma abin har a zuciyata yana damuna.
Suna bin mutanen da suka san fans dina ne ko makamancin haka su tura masa wakata tacikin WhatsApp a matsayin nine.
Su kan sami waka ta daya sai su juya ta su turawa sama da mutun dari ta WhatsApp azuwan nine.
Jarumin ya kara da cewa babban abin da yake bata masa rai shine, Bayan sun turawa wakar sai su tura hoton motata da na taba hatsari suce wai ina bukatar taimako a matsayin mine.
Sakin waka yace ya saka naira muliyan daya ga duk wanda ya samo masa wannan bata garin.