Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Wani sabon al’amari ya bulla akan naiman taimakon al’umma ga jinyar jarumin kannywood Sani Garba SK

Kamar yadda wasu daga cikin ku suka sani a kwanakin baya jarumin masana’antar kannywood “Sani Garba SK” Allah ya jarabce shi da jinya wanda har jarumin ya bayyana a cikin wata bidiyo wana naiman taimakon al’umma.

Advertising

TO a wannan lokacin ma Ficacciyar marubuciyar nan wato “Fauziyya D Sulaiman” wanda shuga ce a kungiyar nan ta nemawa gajiyayyu da marasa galihu taimako.

Ta wallafa wani sabon labari akan jarumin masana’antar kannywood wato “Sani Garba SK” wanda a cikin labarin take nuna cewa, wasu daga cikin jaruman masaana’antar kannywood sun bada taimakon su ga jarumin.

Ga dai wallafar da Fauziyya D Sulaiman tayi a shafin nata akan taimakon da aka yiwa jarumi Sani Garba SK.

Advertising

Ta fara da cewa.

WASU DAGA YAN FIM SUN TAIMAKAWA SANI SK
Mutane suna ta turo min wannan video na Sani Sk akan mu taimaka masa, to magana ta gaskiya a kwanakin baya ma mun yi posting Sani Sk kuma wasu daga cikin yan fim sun taimaka masa kuma suna kan ci gaba da taimala masa da al’umar gari, sai dai cutar shi mai cin kudi ce wato ciwon sugar da ciwon hanta
.

Yanzu haka @abdulamart_mai_kwashewa ya Bashi Dubu Dari biyar, ya sa kuma an kai shi asibiti, Hadiza Gabon ta bashi Dubu Dari Biyu da Hamsin, Ali Nuhu ya bashi Dubu Dari, Aisha Tsamiya Dubu Dari, da wasu da yawa da suka bayar daga masana’antar Kannywood din, muna adduar Allah ya saka musu da alkairi.

Kamar yadda muke fada ciwon Sani Sk ciwo ne mai cin kudi, Yan fim suna iyakacin kokarinsu, amma kuma al’umma dan’uwanku ne musulmi Wanda wannan yan’uwantakar ta fi ta sanaa za ku iya taimakawa ba tare da cin mutunci kowa ba.
Allah ya ba shi lafiya.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button