Abubuwan da baku saniba a game da mawakan da suka fara rere waka a kannywood.
Fitatun mawakan Hausa wanda ba kowa ne yasan sune suka fara rera waka a cikin fina finai ba.
Dalilin haka Hausa daily News ta kawo muku jerin mawakan da suka fara rera waka a cikin film.
(1) Mawaki na farko shine Musbahu M Ahmad Kamar dai yadda wasu suka sani wannan mawaki yaya ne ga fitaccen Mawaki nazir sarkin waka da kuma babban darakta mal aminu saira.
Musbahu yana daya daga cikin shahararrun mawaka wanda Masana’antar Kannywood ba zata manta dasu, wannan mawaki shima ya kwashe kimanain shekaru fiye da shirin yana bada tasa gudumuwar acikin Masana’antar Kannywood.
Bayan rera wakoki da musbahu yakeyi yana kuma fitowa a matsayin jarumi acikin finafinai irin su film din Kansakali, Sangaya, Samodara da sauran su.
Acikin wakokin da musbahu ya rera wanda suka shahara sun hada da wakar film din Kansakali, Hayaki, Allura da zare, sannan kuma sai wakar film din sangaya wacce wannan waka itace a matsayin bakandamiyar shi.
Sannan film din sangaya yana daya daga cikin Finafinan hausa da ake alfahari dasu har a wannan lokaci domin kuwa ya daga darajar Masana’antar baki daya.
Zaku iya sauraran ragowar mawakan acikin wannan Bidiyon dake kasa.