An sami gawar wani jami’in gwamnati bayan EFCC ta bukaci yazo-labarin Hausa.
An tunanin wani babban mutun a gwamnatin tarayya daya kai kusan matakin mataimakin Darakta ya hakala kansa ta hanyar rataya bayan da Hukumar ta EFCC ta bukaci ya zo ofishin su.
Wasu bayanai na cewa ranar da Hukumar ta EFCC mai yaki da Cin hanci da rashawa ta Nigeria ta bukaci mutumin mataimakin Darakta ne a Hukumar ta bunkasa makamashin zamani wato (NABDA) ya ziyarci a ofishinta da ke Abuja ne aka tsinci gawar tasa.
Rahotanni na cewa An tsinci gawar Christopher Orji, tana lilo wanda alamu nanuni da cewa rataye kansa yayi a cikin jerin gidajen ma’aikata gwamnatin, Ana zagin ya rataye kansa ne ranar Litinin 30 ga wata Agusta a Abuja.
Hukumar (NABDA) tace har zuwa yanzu Yan sanda na cigaba da bincike a game da mutuwar mutumin.
Majiyoyi a hukumar ta NABDA sun ce, babu yadda za a yi a ce mutumin ya kashe kansa, tunda bai bar wata takarda da ke nuna hakan ba a gidan.
Har izuwa yanzu dai mai magana da yawun hukumar ta NABDA, Nkiru Amakeze yace, ba’a sami tabbacin abinda yasa ya haka kansa ba.
Ku cigaba da kasan cewa damu a koda yaushe domin samun labarai masu inganci.