Jaruma kannywood Rayya ta Bayyana irin kalar Mijin da take so-Labaran Hausa
Sharariya kuma fitacciyar jarumar fina-finan hausar nan Surayya Aminu wadda aka fi sani da Rayya ta bayyana cewa a kasuwa take tana neman miji domin tayi aure.
Ga duk wanda yake kallon fina finan hausa Bazai kasa san jaruma Rayya ba, Musamman yadda take taka rawar gani a shirin da tashar arewa24 kea hasakawa me suna (Kwana chasa’in)
KARANTA KUMA: Kyan da yagaji uban sa/ Dan marigayi Ibro ya tsinduma cikin kannywood.
Jaruma Rayya ta bayyana cewa a shirye take ga duk wanda yake so da kaunarta tsakani da Allah zai aure ta, kuma shi aure lokaci ne “ina sa ran nayi aure nan bada jimawa ba cikin ikon Allah” a cewar jarumar
Idan zaku iya tunawa dai a kwanakin baya a wata tattaunawa da gidan Radio Freedom tayi da abokin aikin Rayya jarumi Yawale ya bayyana cewa a shirye yake kuma zai iya auren Rayyan a zahiri.
Sai dai a wancan lokacin jaruma Rayya ta bayyana wa Gidan Radio Freedom cewa abu biyu ne zai hanata auren Yawale, Na farko yana da aure ita kuma bata son kishiya, Sannan Yawale bashi da kudi ita kuma mai kudi take so.
Amma daga bisani jaruma Rayya ta sanar da janye wannan kalamai a shafinta na kafar sada zumun ta.
Jaridar mu ta Hausadailynews Tayi yinkurin jin ta bakin Rayya akan janye wannan batu da Jaruma ta janye amma bamu sameta a wayab.
Ku kasance damu domin samun manyan labaruka.
One Comment