Advertising
Advertising
Uncategory

Naziru ka tona asirin ‘yan kannywood ka rantse da Allah kai ma baka taba lalata da wata ba, martanin Fati Slow

Jarumar masana’antar kannywood Fati Slow ita ma ta tofa albarkacin bakin ta akan maganar da Naziru Sarkin waka ya jefe su da ita, na cewa sai anyi lalata da ‘yam mata sannan ake sanya su a shirin fim a masana’antar kannywood.

Advertising

Wanda ita ma jaruma Fati Slow ta soki Naziru Sarkin waka da cewa, shi ma ya rantse da Allah bai tafa neman mata ba tun da yake.

Sannan jaruma Fati Slow ta bayyana cewa, ita tun da take babu wani Furodusa ko Darakta da ya taba neman ya kwanta da ita kafin ya sanya ta a shirin fim din sa.

Jaruma Fati Slow ta bayyana cewa:

Advertising

Gaskiya ba zan boye maka ba abinda kayi gaskiya kayi shirme kuma baka kyauta ba abinda kayi, duk wadanda kuke goyon bayansa a
hankali zaku gane abinda muke nufl.

Kun zo kun tonawa mutane asiri a shafukan sada zumunta, kun zo duk abinda ake yi a Kannywood muna rufawa kan mu asiri kun bayyanawa duniya.

Allah kadai ya san irin bakaken maganganun da aka dinga gaya mini a shafukan sada zumunta, ashe haka kuke dama, ashe baku da sirri, sai kun nemi mace kuke saka ta a flm?.

Wallahi al’umma ya fadi son ransa ne tunda nake a Kannywood ba’a taba yi mini sallamar wulakanci ba, kuma wadannan matan da kake
fada idan zaka rantse da Allah do wacece baka taba nema a ciki ba ko kuma kace baka taba neman wata a Kannywood ba.

Ka na da ilimin addini dana boko yaya za’a yi ka fito kana irin wadannan maganganun? Wallahi
kalIon babban mutum nake yi maka, bai kamata ka fito kayi wadannan maganganun ba.

Kana tunanin cewa mutane za su soka sabida wannan maganar da kayi? ai kudin goro za’a yi mana baki daya, ya kamata ka fito kafar
sadarwa kayi magana, bai kamata abinda kayi ba kana da ilimi daidai gwargwado.

Wannan shine martanin da jaruma Fati Slow ta maidawa da Naziru Sarkin waka akan maganar da ya fada a kan ‘yam matan kannywood.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button