Abubuwan da baku sani ba a game da jaruman kannywood guda Hudu.
Shahrarun jarumai Guda Hudu wanda suka shigo daga ketare suka fada Masana’antar fina finan Hausa na Kannywood.
Hausa daily News tayi kokarin kawo muku jaruman da kum kasashen da jaruman suka fito.
(1) Rakiya Moussa wannan jaruma haifaffiyar kasar Niger ce sannan kuma diya ce ga shahararren mawakin nan kasar niger watau Moussa pousi.
Rakiya Moussa itama ta baro kasar ta ta niger izuwa Nigeria, domin ta shiga cikin Masana’antar shirya finafınan hausa, jarumar tayi fice ne acikin film din Aisha Humaira wanda suka fito tare da jarumi adam zango inda jarumar itace taja ragamar film din.
Hakan yasa masoyanta suke mata lakabi da Aisha humaira, amma ba kowa yasan cewa itace ta fito acikin film din Aisha humaira ba kasancewar a yanzu yanayin ta ya matukar canzawa.
Bayan film din Aisha humaira jarumar ta kara fitowa acikin film din Maijego inda shima wannan film ta taka rawar gani ba kadan ba.
Bayan film din maijego jarumar taja baya ga fitowa acikin finafinai, inda ta koma fitowa acikin bidiyon wakoki tare da manyan mawaka irin su Hamisu breaker, Garzali miko da sauran su.
KARANTA: Jaruma kannywood Rayya ta Bayyana irin kalar Mijin da take so-Labaran Hausa
(2) Jaruma ta hudu it tumba Abubakar wacce akafi sani da tumba gwaska itama wannan Jaruma haifaffiyar kasar niger ce, ta kuma shigo cikin Masana’antar Kannywood a shekara 2013.
Sannan kuma tayi fice ne acikin film din gwaska na jarumi Adam zango, hakan yasa ake mata lakabi da tumba gwaska.
Bayan nasarar data samu a film din gwaska ta kara fitowa acikin finafinai irin su Basaja Takun Farko, A Cuci Maza, Basaja gidan yari da sauran su.
Zaku iya kallon sauran Bidiyon jaruman a cikin wannan Bidiyon.
One Comment