Labaran Kannywood

Dubi jerin Jaruman kannywood din da suka cimma abin alkhari a rayuwar su.

Hausa daily News tazo muku da fitatun jaruman Masana’antar kannywood wanda a yanzu haka suke dakin mazajansu.

Da yawa mutane na na kallon matan fina finan hausa a matsayin wanda bau iya zaman aure ba.

Hakan yasa wakilin mu ya shiryo muku jarumai biyar wanda a yanzu haka auren su yay albarka.

Ga jerin jaruman daga nan kasa.

Muhibbat Abdulsalam itama tsohuwar jarumar Kannywood ce kuma tayi fice ne acikin shekara ta 2004 ta taka rawar gani sannan ta bada gudumuwa ba kadan ba a Masana’antar Kannywood.

Jarumar tayi aure a shekara ta 2009 inda ta auri hassan giggs fitaccen mai bada umurni, Muhibbat abdulsalam itace mace ta farko da take bada umurni acikin Masana’antar Kannywood wanda hakan ya biyo bayan taimako da take samu a wajen mijinta.

Wannan aure nasu yayi Albarka inda sun kwashe kimanin shekara goma sha biyu a tare, inda Allah ya azurtasu da haihuwar yara hudu mata, Muna fatan Allah ya kara hada kansu ya basu zaman lafia ameen.

Abubuwan da baku sani ba a game da jaruman kannywood guda Hudu.

Mansurah isah Abubakar, itama ta jima a Masana’antar Kannywood ta taka rawar gani acikin finafinai da dama irinsu film din Bil’adama, Gurnani, Jurumai, da kuma Turaka. 14.05.2

Jarumar itace ta kirkiri gidauniyar Todays life foundation, wannan gidauniya tana taimakawa mutane Mabukata, yara marayu, da kuma nakasassu, jarumar itama tabar hakar film ne a shekara ta 2007.

Inda ta auri sani musa danja wanda shima Fittaccen jarumi a Masana’antar Kannywood, suna daya daga cikin

jarumai da suka auri junan su sannan kuma auren yayi albarka, inda a yanzu kun kwashe shekara goma sha 14 a tare.

Allah ya azurtasu da haihuwar yara hudu maza uku da mace daya, Muna fatan Allah ya kara hada kansu ya kuma basu zaman lafia ameen.

Zaku iya kallon ragowar jaruman a Bidiyon dake kasan wannan rubutu.

cikaken bayani a game da jaruman

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button