Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jaruman kannywood da suka Auri junan su/ Daga baya kuma Aurn ya mutu.

Hausa daily News.Com ta Hada muku jerin Jaruman Masana’antar kannywood da suka auri Junan su kuma daga baya auren ya mutu.

Advertising

(1) Sani Musa danja jarumi, mai bada umurni sannan kuma shima ya kasance mawaki, ya kwashe shekaru da dama acikin masana’antar kannywood wanda shima yana cikin zubin farko na manyan jarumai da suka dade suna gabatar da harkar finafinai.

Yayi finafinai da dama da sukayi fice irin su Dan zaki, daham, Jarida da sauran su a karkashin fitaccen kampanin su me suna 2effects empire.

Sani danja yana daya daga cikin jarumai wanda ba’a finafinan kannywood kawai suka tsaya ba domin kuwa shima yayi fice a finafinain turanci da akeyi a kudancin nigeria.

Advertising

Also read: Ya yan jaruman kannywood da suke so sufi iyayen su suna a Masana’antar.

Sani danja ya auri mansurah isah wacce itama fitacciyar jaruma ce, an daura auren nasu a shekara ta 2007 duk da kasancewar jarumi sani danja ya dade yana soyayya da Jaruma Maryam jankunne kafin soyayyar su da mansurah.

Amma Allah bai nufa matar sa bace, Maryam itama ba boyayya bace a masana’antar kusan dukkan wanda ya dade yana kallon finafinan hausa to bazai mance da fuskar taba.

Sani danja da mansurah suna daya daga cikin jaruman kannywood da suka auri junansu sannan kuma auren yayi karko inda sun kwashe kimanin shekaru 14 a tare.

Inda Allah ya azurtasu da haihuwar yara guda 4, mace daya da maza 3, Hakan yasa suka zama abin kwatance inda mutane da dama da sauran abokan sana’ar su suke jinjina masu.

Also read: Gwamnati: Wata mumunan Ambaliya ruwa ta mamaye wasu manyan ban garori a jigawa.

Sai dai acikin shekarar nan ta 2021 jaruman sun samu matsala inda har hakan ta kaiga rabuwar auren nasu, duk da kasancewar wannan ba shine karo na farko ba da suka rabu, sai dai ba wanda yasan dalilin rabuwar tasu.

Amma a yan kwanakin nan mun samu labarin cewa jaruma mansurah isah ta koma dakin mijinta, a karshe muna masu fatan Alkhairi Allah ya daidaita tsakanin su ya kuma basu zaman lafia me dorewa.

Zaku iya kallon Bidiyon dake kasan wannan rubutu dan nan jin bayanin ragowar jaruman.

Ga Bidiyon bayanin jaruman

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button