Advertising
Advertising
Labarai

Allah ka kare mu: Kalli ta hanyar da ake aikawa ‘Yan ta’addan cikin Daji makaman yaki

Shahararran marubucin nan Datti Assalafy ya wallata wata bidiyon yadda wani jirgin sama yake saukewa ‘Yan ta’addan cikin Daji makanai, tare da wani rubutu inda a cikin rubutun yake cewa.

Advertising

Babban sako cikin bidiyo, jirgin sama mai saukar ungulu (Helicopter) ya sauka a tsakiyar Daji dauke da makamai da kayan masarufi ya kaiwa Barayin daji masu garkuwa da mutane.

Sannan kuma zaku ga yadda Barayin Dajin suke sauke makaman da sauran kayan daga cikin jirgin, sunayi da hanzari, wanda Barayin sun kasance Fulani ne kamar yadda dama ake zargin Fulani ne suke yin garkuwa da Mutanen.

Abinda ake fada shekara da shekaru cewa: Jirage masu saukar ungula suna sauke makamai da sauran kayan bukata ga Barayin Daji, bidiyo gashi nan a zahiri babu wani tawili.

Advertising

Sai dai ni Datti Assalafiy bani da tabbaci ko a ina ne wannan mummunan cin amanar tsaron kasa yake faruwa, kalubale gareka Maigirma shugaban kasar Nigeria Muhammadu Buhari.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button