Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Ya yan jaruman kannywood da suke so sufi iyayen su suna a Masana’antar.

Hausa Daily News tayi muku babban nazi a game da wasu daga cikin yayan jaruman kannywood wanda ake sa ran zasu maye gurbin iayayen su a Masana’antar.

Advertising

(1) lman Sani Danja ‘ya ga Sani Musa Danja ce wadda ta shiga Masana’antar tun tana da kananan shekaru wadda a yanzu haka tana daya daga cikin wanda suke fitowa a Film dinan me dogon zango Gidan danja.

Tauraruwar Iman ta fara haskawa ne a wani Film mai suna Akila na kamfanin 2effect wanda a wannan Film tai suna.

(2) Ahmad Abdulmumini tantiri wanda dane ga fitaccen jarumin kannywood ilyasu Abdulmumini tantiri, Ahmad shima yana daya daga cikin jerin fitattun yara jarumai wanda shima ya samu kyaututtuka da dama.

Advertising

Yayi fina-finai da dama inda yayi fice acikin film din “Danzaki” Ahmad shima yana samun taimako ta wajen mahaifin sa hakan yasa shima ya shigo cikin jerin yara jarumai wanda anan gaba zasu maye gurbin mahaifansu a masana’antar kannywood.

(3) Ahmad Ali nuhu daya daga cikin yara jarumai wanda tauraronsu ke haskawa, duk da kasancewar fitowar sa a finafinai taja baya ba kamar yadda ya fara ba.

Ahmad ya fara harkar film tin yana karamin yaro wanda be wuce shekara bakwai ba, film dinsa na farko da yayi fice shine fim din “Dattijo” da kuma sauran finafinai irin su Zuri’a, Uba da da, dan Almajiri, kara da kiyashi da dai sauransu.

Ahmad ya samu nasarori da kyaututtuka da dama a kannywood wanda hakan yazo ta dalilin taimako da yake samu a wurin mahaifinsa, Wannan ne yasa ya zama na daya acikin jerin yara wanda tauraronsu zai mamayi kannywood anan gaba.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button