Yan Bindiga na neman sulhu da Gwamnatin Zamfara.
Gwaman Jahar Zamfara, Bello Muhammad Matawlle yace yan bindiga sunji luguden wuta sun fara son ayi sulhu.
Bello Matawall yace Gwamnatin jahar tasa baza ta sake yarda da yin sulhu da syan bindigar ba sabida a baya sunsha karyar yan bindiga.
Ya kara da cewa ina Gwamnatinmu ba za ta taba amincewa da sake wani sulhu da wasu yan bindiga ba Sabida a baya sunyi watsi da zaman, a cewar Gwamnan.
Gwamnan yay kira ga mutanan gari da suyi hakuri subi tsarukan da sojoji suka kafa domin aga an kawo karshen yan yan bindiga, Ya kuma kara da cewa yanzu haka wasu daga cikinsu sun fara guduwa zuwa wasu Garuruwan sabida Luguden wuta.
Matawalle ya ja kunan ’yan siyasa Jahar da su ji tsoron Allah su daina tmakawa wa ’yan bindigar ta kowacce yanayi,
Musamman ta hanyar rabawa mutane babura wadanda su kuma daga baya suke sayarwa da ’yan bindigar don ci gaba da aikata Fasa kwari a garin.
A kwanan baya dai a jahar Katsina yan bindiga suka addabawa Jahar, Gwamnatin tasa aka dakata da siyar da mashin me kafa biyu kirar boska sabida yan bindiga suna siya suyi aiki dashi.
Haka kuma suka dakatar da siyar da wata wayar salula da ake mata lakabi da Burin dan fulani.
One Comment