Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Yan Jaridu sun fusata akan maganar da Sarkin waka ya fada a Shirin Film din Labarina.

Da yawan ‘yan jarida sun mayar da martani ga kalaman da Shahararren mawaki Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙa) ya furta a kan ‘yan jarida a cikin Shirin Film dinan mai dogon zango “Labarina”.

Advertising

A satin daya gabata an haska shirin na 11 wanda aka haska a jiya Juma’a data gabata. An nuno wani matashin dan jarida ya je ofishin Naziru Sarkin Waka don neman jarin bayani a kan sabuwar wakar da daya daga cikin yaransa ta saki wato Sumayya wada akafi sani da (Nafisat Abdullahi) ta fitar mai taken “Dawo-Dawo” Wadda ta rerawa Saurayin ta Mahmud.

Dan jaridar yazo ofishin sai ya tarar Naziru sarkin waka na shirin fita Unguwa sai yace masa ranka ya dade inaso In dan maka wasu tambayoyi a game da wakar da Sumayya tayi.

KARANTA: Naziru sarkin waka Dawo Dawo

Advertising

Dan jaridar yazo ofishin Naziru Sarkin waka, dan samin labari akan waye Mahmud wanda Suayya tayiwa waka. Ya wa Sarkin Waka ‘yan tambayoyi, shi kuma ya ce masa ba shi ne ya ke da hurumin bayar da amsa ba, sai dai ya yaje ya tambayi Sumayya.

Suna shirin rabuwa, Sai Sarkin waka yace a bawa dan jarida kudin mota ya tafi, Ba suyi wata sallamaba Sakin waka ya haye motar sa ya fice.

Wannan magana tawa ‘yan jaridu zafi matuka, Inda suma suka fara ajiya kalamai kala-kala a shafukan su a game da abinda Sarkin waka yace wa dan jaridar.

Ga irin post din yan jaridun kadan daga ciki. suka wallafa da kuma masu tofa albarkacin bakin su.

KALAMAN ‘YAN JARIDA
KALAMAN YAN JARIDA
MASU TOFA ALBARKACIN BAKIN SU
MASU TOFA ALBARKACIN BAKIN SU

Advertising

23 Comments

  1. Wannan ni a nawa raayin banga wani cin mutunci ba saboda hakan tana faruwa kaje yiwa mutum interview yabaka brown envelope so dan naziru yace anemamasa kudin mota ai ba laifi bane ko kawai inda nake ganin anci mutuncin aikimmu shine yakamata a bawa dan jarida lokaci domin yashiga har ofishin naziru ba wai ya tareshi akan hanya ba saboda idan Ka tare mutum akan hanya komai ze iya fadama

  2. Muma zamu cigaba da an hankalin mutane musamman masoyan mu, da a daina kallon Shirin, ai sai an kalla suke yin sabo Kuma suke samun kudi, na zaci tsakaninmu da Yan fim Babu irin wannan Amma Aminu Saira ya karyata tunaninmu akan hakan. Mtwwww

 1. Wallahi wash lokutan sai ince my Arewa kodai wasunmu kwakwalen dabbobine damu😢
  Bamuda aiki sai Hassada da hantarar juna🙁
  Karamin Abu indai Dan uwanmu Dan Arewane saimu maidashi babba
  Sannan babban Abu idan bamu aka taba ba saimu maidashi bakomaiba😔
  ALLAH YASA MUDACE

  1. Wannan shine gaskiyar lamari dukda nima yarone amma gsky abun danake ta fahimta kenan a halin yanzu social media abunda akasa a gaba kenan Allah ya shirya
   Yakuma shirye munafukai masu tsugudidin zance irin wannan Amin

 2. Kuna wani gayawa naziru magana nidai Banga ta inda aka hulakanta Dan jaridava sabida duk tambayar da yy Masa yabashi amsa Kuma yagayamasa inda yakamata yaje yanemi Karin bayani ..akarshe Kuma yy Masa alkhairi ..Amma Kuna tacewa anci mutum cinku yakamata Wanda bai kalli wannan film yaje yakara gani Dan gani yakuriji

 3. Agaskiyar magana da yawan mutannamu sunada jahilci ko nace suna jahiltar Abu ya kamata idan mutum ya jahilci Abu yadaina yanke masa hukunci lokaci guda.

 4. Labarina wasan kwaikwayone na so yadda akaba sarkin waqa umarni haka zaiyi cecekuce sai ayiwa Companin Saira Movies.

  1. Kuna Ina alokacin da Yan siyasa ke cin zarafin Yan jaridun naku wni lokacinmma harda duka da barazanar kisa, Amma dukkanku babu Wanda yafito yace shi Dan jarida ne kokuma Mai Kare hakkin aikin jarida,, Sai awasan kwai kwayo kukafi iya Kare aikin jarida don Allah mudunga nuna ilimi ne yasa ake kiranmu Yan jaridun ba hauka ba

 5. Idan Da Ace Bai Taras da Naziru Zai fita ba shine Zai Zama laifi Amma Idan Dan Siyasa ne baza,Ayi Masa Wannan Tererenba munason Yan Jarida da Kuma Aikinsu Amma Wannan Maganar ta Naziru Batakai A Gaggaya Masa Magana Haka ba Allah ya Kyauta

 6. Amma mutane suna da matsala wlh wannan abun da yafaru awannan scene din kuskuren awajen editing ne kuma ina Baku hakuri amadadin #Amunu saira and naziru sarkin waka Amatsayi na na dan jarida

 7. Ba Naziru ne ya wulakanta yan jarida ba sai dai wasu daga yan jaridar suka wulakanta Kansu da kuma aikin su, suna iya binciko kankanin laifin talaka su zuzuta shi sannan su 6oye manyan laifukkan manyan kasan nan tareda yan siyasa saboda Neman na goro. Dan jarida mutum ne mai mutakar amfani ga al’umma a lokacinda aikin jarida na matsayin sa. Jaridun kasar nan sun binciko kuma sun wallafa yan taada dake addabar jamaa amma har yanxu bamuji anlalube manyan dasuka saka su. Sannan Kayan abinci dana masarufi suna kara farashi amma haryanxun babu jaridar Kazan nan data binciko dalilin Karin sannan kuma daga yan kasuwane Karin yake koko daga company

 8. Toohhh ehmm ana wata ga wata wannan ai zan’iyacewa bawani abun mamakibane don wai yan jarida sunfadi hakan dunminkuwa yan Nijeriya ne, that is our habit, dominkuwa akodayaushe dan Nijeriya soyakeyi wani daga cikin yansiyasa kokuma wani fitaccen mutum yayi wani kuskure kokuma tuntuben harshe ayayin magana tohfa shikenan yasamu tacewa don haka wannan sunayine don wata manufarsu

 9. Wallahi ko a zahiri duk Dan jarida da zaiyi hira da wani sai bada wani abu. Soboda haka kudai na tonama kanku asiri.

 10. Balefi Bane Dan yace Abashi Kudin Mota Kyautatawace Kawai dai Shi Naziru Bebiyo Ta Hanyar Data Daceba Saboda Yayi Abin Cikin Izza Da Nuna Isa.

  Sannan Kuma Shikansa Dan Jaridar Anawa Ganin Bekamata Yaje Har Office Akan Wannanba Saboda Ba Serious Issue Bane,A Waya Yakamata Yakirasa Idan Shiyakeson Yayiwa Magana Kokuma Sunemi Ita Nafisar Dansuji Daga Bakinta Ina Nufin Suyi Program Da Ita Akan Wakar Kaga Anan Zasu Kara Samun Wasu Amsoshin Wanda Tunaninsu Bekawoba.

 11. A gaskiya bawani cin zarafi anan rahinfahimta ce kawai aka samu Amma idan ma wani Yana ganin an ci masa zarafi to don Allah a yafe wannan fa Shiri kawai.

 12. Toh Allah ya kyauta. Matsalarsa daya kullum yanason yaga ya nuna gajiyawar wani, haka kwanan baya akai da Yan crypto. To pls wai Mai ke jawo hakane ? In wannan wasane (film) crypto fa tunda ba wani malami dayazo da fatawar hani akai, gaskia adinga kula wajen neman ilimin Abu kapin ayi Masa hawan mikiya. Allah yasa ya gyara NAZIRU MUHAMMAD MAWAKI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button