Labaran Kannywood

Allah yayiwa fitaccen Mai daukar hoto a kannywood Ahmad tage Rasuwa.

Innalillahi wainnailaihi rajiun A yau ne muka samu labarin rasuwar fitaccen mai daukar hoto sannan kuma jarumi a Masana’antar Kannywood, watau Ahmad tage.

Bayan daya sha fama da gajeriyar rashin lafia, kamar dai yadda shafin Kannywoodcelebrities suka wallafa labarin rasuwar tasa a shafin nasu na instagram.

Marigayin dai yana daya daga cikin manyan masu daukar hoto a Masana’antar Kannywood, wanda ya dade yana bada gudumuwa.

yayi finafinai da suka shafara irinsu Namamajo wanda suka fito tare da jarumi Adam zango da kuma marigayi rabilu musa ibro muna fata Allah yaji kansa yayi masa rahama ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button