Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Bukukuwan Jaruman Kannywood din da suka Angwamce a 2021.

Jaruman Masana’antar Kannywood da suka angwance da kuma wanda suka Amarce a cikin shekar 2021.

Advertising

Kaman yadda muka saba dai muna kawo muku manyan batutuwan da suka shafi Masana’antar Kannywood.

(1) Jaruma ta Farko itace Zarah Muhammad da akafi sani da Zarah Diamond fitacciyar jaruma wacce haifaffiyar kasar niger ce itama wannan jaruma ta amarce acikin watan Augusta shekara ta 2021.

KARANTA: kannywood actress Rahama Sadau has been in a state of shock since she was fired from the industry

Advertising

Sai dai auren nata yazo ne amatsayin bazata kasancewar suma kansu abokan sana’ar ta ba kowa yasan da batun auren ba, sannan har yau dai babu wata majiya ko wani daya san mijin da ta aura.

Inda a yanxu hakama account dinta na Instagram ta boyeshi, sannan akwai ayyuka dayawa wanda bata gama ba sai dai ta bada hakuri ga producers da directors.

Jaruman Kannywood sun tayata murna ta hanyar wallafa hotunan ta a shafi kansu na sada zumunta suna mata fatan alkhairi, Muna fata Allah ya bada zaman lafia, ya kuma sa wannan aure yayi karko har iya karshen rayuwarta.

KARANTA: Allah yayiwa fitaccen Mai daukar hoto a kannywood Ahmad tage Rasuwa.

(2) Jarumi na biyu shine Garzali Mika’ilu Mai Lema wanda akafi sani da Garzali miko, Jarumi fitaccen mawaki sannan kuma gwani a wajen taka rawa.

Garzali miko yana daya daga cikin jaruman Kannywood da suka angonce tare da amaryar tasa me suna Habiba umar dikwa acikin watan augusta shekara ta 2021.

Tarin jaruman kannywood maza da mata sun halarci wannan biki, ayayin da wasu suke ta wallafa hotunan jarumin da amaryar tasa a shafikansu na sada zumunta.

Acikin shagulgulan biki da akayi an buga kwallon kafa tsakanin Team din Bangaren amarya dana ango harma dana jarumi ali nuhu da kuma team Na abdulamrt mai kwashewa.

Manyan jarumai da suka halarci wannan daurin aure sun hada da jarumi Ali nuhu, Adam a zango, Lawal ahmad, salisu S fulani, kb international da sauran su, A karshe muna masu fatan Alhairi Allah ya basu zaman lafia.

Zaku iya kallon Bidiyon dake kasan rubutu dan Ganin ragowar jaruman.

Kalli bidiyo Ragowar jaruman

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button