Hanyoyin da yan bindiga zasubi wajen gujewa luguden wuta: Sheikh Ahmad Gumi.
‘Yan bindiga sun tabbatar da cewa luguden wuta ta jiragen yaki ba zai yi tasiri a kansu ba Inji Sheikh Ahmad gumi.
Malamin yace ‘yan fashin daji sun san hayoyin da suke bi wajen gujewa luguden wuta.
Malamin da ke shan caccaka, ya shawarci ‘yan sanda da Sojoji kan dole ne su hada kai da makiyayan yankunan da ake abun Domin samun sauki abin.
Sheikh Ahmad Gumi ya ce ‘yan bindigan sun zama kwararru waje Gujewa duk wani Bam da sojojin Sama zasu Hullo musu, Wannan dalili ne yasa baza’a iya kawo karshen suba.
Wani Rahoto da Hausa Legit ta fitar, Sun ce malamin yace:
“Babban abin da baku sani ba shi ne, ‘yan bindigan sun Samo hanyoyin gujewa luguden wuta da ake musu ta sama. Sun sanar dani cewa, za ku iya kashe matansu da yaran su ne kawai ta wannan hara-haren da suke kaiwa.
“Abun da nake nufi shine, idan aka matsanta a garin zamfara, To babu shakka Zasu shiga makotan jihohin Garin daganan kuma ‘yan bindiga zasu zama a ko ina a Nigeria.
Sheikh Ahmad yayi karin bayani inda yace Hanya mafi sauki da za subi shine, Daukar makiyaya wajen shiga lungu da sako, da kuma samun Jami’ai na gari.
“Magana ta gaskiya, cutar ta’addanci da gurbatattun shugabanni, Sune Matsalar matlar da ta addabi al’ummar mu.”
One Comment