Labaran Kannywood

Nasara 6 wada ba wanda ya taba samunta a Masana’antar Kannywood face Rahama Sadau.

Fitacciyar Jarumar finafinan hausa Rahama ibrahim da akafi sani da rahama sadau daya daga cikin manyan jarumai a Masana’antar Kannywood.

Jarumar ta fara harkar film a shekara ta 2013, tayi Finafinai da suka shahara irin su Rariya, mati da lado, kanwar dubarudu, da kuma jinin jikina.

Sai dai jarumar ta fuskanci wasu matsaloli a shekara ta 2015 inda ta fito a wata bidiyon waka tare da wani mawakin hiphop, wanda har hakan yayi sanadiyyar korar ta daga Masana’antar ta Kannywood.

KARANTA: Rahama sadau ta fito a wani Saban Film din Bollywood na Indiya me suna Khuda Haafiz.

Sannan a shekara ta 2020 jarumar ta wallafa wasu hotuna a shafinta na instagram wanda hakan ya jawo cece kuce a tsakanin dumbin masoyanta.

Daukakar jarumar dai ta fara ne bayan korar ta da akayi a Masana’antar ta Kannywood inda a yanzu itace jarumar Kannywood ta farko data samu nasarori fiye da sauran jarumai da suka dade acikin a Masana’antar.

To a yanzu zamu kawo maku jerin Nasarori shida tare da daukaka wanda jaruma rahama sadau ta samu fiye da sauran jarumai da suka jima a Masana’antar.

kannywood actress Rahama sadau talks about wedding dress of Bichi Emire’s doughter

1) Jaruma rahama sadau itace jaruma ta farko da tayi fice a finafinan Nollywood da ake gabatar dasu a kudancin Nigeria.

(2) Tana daya daga cikin jaruman Kannywood da sukafi kowa samun kyaututtuka da lambobin yabo.

(3) Itace mace ta farko a Kannywood data samu daukaka da nasarori fiye da sauran jarumai duk da kasancewar bata kwashe wasu shekaru masu yawa ba a Masana’antar.

(4) Jarumar tana daya daga cikin manyan jaruman Kannywood da sukafi kowa yawan mabiyan a shafikan su na sada zumunta, inda a yanzu tana da mabiya da suka kai 2.5M a shafin ta na instagram.

(5) Sannan itace ta kirkiri gidauniyar nan me suna rayofhope, gidauniya da take tallafawa mabukata gajiyayyu da kuma marayu.

(6) A karshe jaruma rahama sadau itace jaruma ta farko da ake tunanin zata fara fitowa acikin fina-finan kasar indiya, kamar dai yadda jarumar ta wallafa wasu hotuna a shafinta na instagram inda ta bayyana cewa suna tsaka da aikin shirin.

Jarumar dai tasha yabo da kuma adduo’i a wajen dumbin masoyan ta, kasancewar wannan shine karo na farko da wani jarumi daga cikin Masana’antar Kannywood zai fito acikin finafinan kasar india.

Hakan yasa Dumbin jarumai irin su Ali nuhu, Fati washa, Amal umar da wasu abokan sana’ar ta dake kudancin nigeria da sauran masoyan ta suka tayata murna da fatan Alkhairi a shafinta na instagram akan wannan daukaka da nasara data samu.

Zaku iya kallon ragowar jaruman in kun danna Bidiyon dake kasan rubutun.

Bidiyon Ragowar Jaruman

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button