Labarai
Wata mota kirar kwantena tayi ajalin wani dan karota
Wata mota kirar kwantena tayi ajalin wani dan karota a kan titin zone one dake karamar Hukumar Gwale kan titin BUK road.
Advertising
Wanda ganau ne ba jiyau ba sun shaidawa wakilin Hausa Daily News cewa:
Dan karotar ya tsayar da mai Motar kirar kwantena yaki tsayawa, Inda dan karotar ya dane a jikin Murfin motar Ya wado suka takashi nan take rai yay halinsa.
Mai motar daya take jami’in Karotar sun bar motar a wajen sun cika wandonsu da iska.
Advertising
Amma jami’an Hukumar kula da ababen hawa ta ‘FRSC’ Sun chafke motar kirar kwantena.
Munyi kokarin jin ta bakin shugaban Hukumar amma be amsa wayarba.
Advertising
Allah yajikan sa