Labarai
Da Dumi Dumi: Dreban daya halaka Dan Karota yazo Hannu.
Jami’an Hukumar Kula da hadura ta Nigeria Road safety da Hukumar Karota, Jami’an sunyi Nasarar kama Mutumin da ake zargi da Hallaka dan Karota da mota.
Advertising
Mai magana da yawun Hukumar Nabulisi Abubakar kofar na’isa ne ya tabbatar da hakan a wata zantawa dayay da manema labarai.
Nabulisi yace tuni Jami’an suka mika wanda ake zargi wajen yan sanda domin gudanar da kwakwaran bincike.
A jiya ne wani matukin babbar motar kwantena yay ajalin wani jami’in Karota a kan titin Zone one karamar Hukumar Gwale dake kano.
Advertising
Dan karotar ya tsayar da mai Motar kirar kwantena yaki tsayawa, Inda dan karotar ya dane a jikin Murfin motar Ya wado suka takashi nan take rai yay halinsa.
Advertising
One Comment