Fitatun Jaruman Kannywood wanda suke malaman makaranta.
Hausa Daily News ta kawo muku shahararun jaruman kannywood wanda suke malaman makaranta ne.
Munsan mai karatu zai so yaji suwaye malaman kuma wane makarantu suke koyarwa.
(1) Kabir Abubakar Aliyu da akafi sani da Kabiru Na kwango daya daga cikin Fitattun jarumai da suka shahara acikin Masana’antar ta Kannywood.
Kabiru nakwango ya dade yana bada gudumuwa a game da harkokin finafinai, sai dai jarumin ya dade ba’a ganinshi acikin finafinai wanda hakan yasa akaita cece kuce akan ya rasu, amma yana nan da ransa.
Dukkan finafınan sa yana gabatar dasu ne abisa koyarwa irin ta addinin musulunci, Mafi akasarin finafinan da yake fitowa duk wa’azi ne da kuma tunatarwa ga al’umma.
Kabiru nakwango yana daya daga cikin Jaruman Kannywood daba kowa yasan cewa malamin makaranta bane, inda yake koyar wa a wata makarantar islamiyya dake dala cikin jahar kano.
(2) Hadiza Aliyu Gabon da akafi sani da Hadiza gabon wannan jaruma haifaffiyar kasar gabon ce, sannan tana daya daga cikin jaruman Kannywood mata da suka samu nasarori da daukake a Kannywood.
Jarumar na samun yabo daga wurin jama’a ganin yadda take taimako ga mabukata da gajiyayyu a karkashin gidauniyar ta me suna HGabon foundation.
Hadiza gabon itama tana cikin jaruman Kannywood da suka kasance malamai inda ta koyar da yaren faransanci a wata makaranta bayan data kammala karatun ta na diploma.
(3) Sadisu Abba sawaba wanda akema lakabi da sani sawaba wannan jarumi haifaffen garin jos ne sannan kuma daya daga cikin manya jarumai.
Duk da kasancewar a yanzu an kwashe wasu shekaru rabon da aga fuskar jarumin acikin finafinai, mutane da dama nata tambaya akan dalilin da yasa jarumin ya daina fitowa acikin finafinai.
Amma dai babu wata majiya da tasan dalilin hakan, sai dai muna tunanin yanayi da Masana’antar ta tsinci kanta na rashin hadin kai, da abubawa na rashin dacewa da suke faruwa yasa jarumin yaja baya ga harkokin.
Shima dai wannan jarumi ya kasance malamin makaranta ne inda ya taba koyarwa a wata makarantar primary dake jahar kaduna.
Mungode da ziyartar Shafin m. Ku cigaba da kasancewa da mu domin zamun zafafan labarai.
2 Comments