Jaruman Kannywood 6 wanda suka rasu aka kasa maye gurbin su.
Har yanzu dai Masana’antar ta Kannywood ta kasa maye gurbin wasu fitattun Jaruman nata kasancewar sun taka muhimmiyar rawa, sannan kuma sun bada gudumuwa ta ko wane bangare acikin Masana’antar alokacin rayuwar su.
Kamar irin su Marigayi Rabilu Musa Ibro wanda ya zama lamba ta daya sannan kuma babban jigo a finafinan Barkwanci.
To hakama acikin shekara ta 2021 Masana’antar ta Kannywood ta kara yin wani babban rashin na wasu Fitattun Jaruman nata, wanda suka hada Tsohuwar jaruma.
Fitaccen mai daukar hoto da kuma mawaki, wanda wannan rashi ya matukar tada hankalin jaruman da Masana’antar baki daya.
KARANTA: Fitatun Jaruman Kannywood wanda suke malaman makaranta.
Marigayiya Hajiya Fatima tarauni wacce akafi sani da Kaka ta bawa acikin shiri mai dogon zango na Dadin kowa wanda gidan talabijin ta Arewa24 take RND gabatarwa.
Allah yayi wannan jaruma rasuwa a jahar kano ran Alhamis 11 ga watan 3 na shekara ta 2021, an kumayi janaizarta a garin na kano kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.
Dumbin jaruman Kannywood da kuma tashar arewa24 sun nuna alhinin su da addua ga marigayiyar na wannan babban rashi nata da akayi Muna fatan Allah yaji kanta ya mata rahama ameen.
KARANTA: Gaskiyar Hotunan Auren adama dawani matsahi
Hajia zainab musa booth tsohuwar jarumar Kannywood wacce mahaifiyace ga maryam booth, Ramadan booth da kuma Amude booth.
Allah yayiwa jarumar rasuwa ne ran 2 ga watan 7 na shekara ta 2021, bayan rashin lafia da tasha fama da ita.
kamar yadda jaruma maryam booth wacce diyace ga marigayiyar ta wallafa labarin rasuwar mahaifiyar tata a shafin nata na instagram.
Anyi janaizarta Kamar yadda addinin musulunci ya tanadar muna fatan Allah yaji kanta ya haskaka kabarinta ameen.
KARANTA: Da Dumi Dumi: Dreban daya halaka Dan Karota yazo Hannu.
Marigayi isyaku forest fitaccen mawaki wanda mutumin jahar kano ne yana daya daga cikin manyan mawakan siyasa a arewa da suka bada gudumuwa ba kadan ba a jamiyyar APC.
Allah yayima isyaku forest rasuwa ran 4 ga watan 9 na shekara ta 2021, bayan da jarumi Ali nuhu ya wallafa labarin rasuwar tasa a shafinsa na instagram.
Shima dai anyi janaiarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar, muna fata Allah yaji kansa ya gafarta masa ameen.
Marigayin wanda yana daya daga cikin manyan masu daukar hoto sannan kuma jarumi a Masana’antar Kannywood.
Yayi fice a finafinan barkwanci da suka shahara irin su film din namamajo wanda sukayi tare da marigayi rabilu musa ibro da jarumi adam zango.
Allah yayiwa wannan jarumi rasuwa ran 13 ga watan 9 na 2021 bayan gajeriyar rashin lafia. Muna fata Allah yaji kansa ya masa rahama da sauran musulmai baki daya.
Allah yayi musu rahama
Allah ya gafarta musu,kuma ya musu rahama
Allah ya jikansu da rahama
Allah ya jikan su da rahama yasa aljannah makoma, yabawa yan uwa da abokan arziki jure rashinsu, musamman kaka ta bawa,
Allah yajikansu
@Hausadailynews Duk inda ka saka video na to dole kayi embedding Vedion sannan ka bada Credit wannan shine Adalci Kuma shine tsari na media, Amma mutum yasha wahalar hada vedio cikin 5min ka dauka ka maidashi text, sannan babu inda ka bayyana cewa ga wurin da ka samu wannan abun, ai hakan bai dace ba Tsakani da Allah.
Duk Sauran bloggers Masu Amfani da vedios daga YouTube suna fadar cewa ga channel dinda take da mallakin Vedion sannan su kumayi embedding vedio.
Allah yasa mu dace.
kana arewa YouTubers?