Advertising
Advertising
Labarai

Asibitin murtala dake kano sun tabbatar da Abduljabar lafiyar kunen sa kalau.

Binciken Asibitin masu fama da tabun kwakwalwa na Dawanau da ke jihar Kano a Najeriya ya ce Abduljabbar Kabara ba shi da matsalar tabun ƙwaƙwalwa.

Advertising

A ci gaba da zaman sauraren ƙarar malamin da ake yi, duka lauyoyin Abduljabbar ba su halarci zaman kotun ba na ranar Alhamis.

Wakilin gidan jaridar BBC ya je zaman kotun ya ce lauyan Abduljabbar ne ya je kotun Barista Haruna Magashi kuma take ya ce ya janye daga wakiltar abduljabbar.

Ya umarci Sauran lauyoyin suma su janye daga kare Abduljabbar shi ya sa dukkansu halarci zaman kotun.

Advertising

Asibitin Dawanau na masu matsalar kwakwalwa ya ce an taɓa kwantar da Abduljabbar a asibitin na tsawon kwana hudu a baya.

KARANTA: Jaruman Kannywood 6 wanda suka rasu aka kasa maye gurbin su.

An taba kwantar da malamin a lokacin daya taba rikici da yan uwansa. na tswawan kwana hudu, amma ba a taɓa yi masa gwaji ba kuma ba a taɓa ba shi magani ba,” in ji mai karanto bayani a gaban Alkali Sarki Yola.

“A sakamakon gwajin kunnen da muka samu daga Asibitin Murtala, an tabbatar da cewa Abduljabbar ba shi da matsalar kunne ko kuma ji ko kaɗan.

Ya tambayi sakamakon Asibitin Murtala da aka kai Abduljabbar domin yi masa gwajin kunne, saboda gaza amsa tambayoyin da aka yi masa a zaman kotun na baya, wanda ake tsammanin ko ya samu matsalar kunne ne.

Alƙali Yola ya ce ya amince da buƙatar lauyoyin Abduljabbar na janye wa daga kare malamin.

Alkhali Sarki Yola ya sake ɗage karar zuwa 30 ga watan sabunta nan.

Advertising

12 Comments

  1. Pingback: viagra canada

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button