Advertising
Advertising
Labarai

Asirin mutanan da suka halaka dan Sanata Na’Allah ya tonu.

An sami nasarar kama mutun biyu wanda ake zargi da halaka Kyaftin Abdulkarim da ga Sanata Bala Ibn Na’Allah sun Shiga hannun jami’an tsaro.

Advertising

Wata majiya tace an kama mutanen da sukai wa Kyaftin din kisan gilla da aka yi wa Dan sanatan mai shekara 36 a gidan sa aka kuma yi gaba da motarsa ta hawa.

Kakakin Rundunar yan Sandan jihar Kaduna ASP Jalige Muhammed ya ce, mutun biyu daga cikin mutanen da ake zargi da halaka Abdulkarim Na’Allah Daya daga cikin su ya gudu inda biyu ke hanun mu.

KARANTA: Ango yayi magana akan Hotuna su da adama dadin kowa

Advertising

Har yanzu Babu cikaken bayani a game da mutanen da ake zargi, Wata majiya tace mutanen da ake zargi yan shekara 20.

Wata majiya mai tushe tace an samo motar mamacin da aka halaka wata iyaka achan kasar Nijar.

Tun a wata Agusta ne aka yiwa matashin matukin jirgin sama kisan gilla a garin Kaduna a gidan sa dake unguwar malali GRA.

Har izuwa yanzu jami’an tsaro na cigaba da bincike a game da lamarin.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button