Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jaruman Kannywood da Suka sauya Akalar su Zuwa ga Masu bada Umurni (Directors)

  1. Mal. Aminu Saira

Na farko shine Aminu Muhammad Ahmad wanda akafi sani da Malam Aminu saira Fitaccen mai bada umurni wanda ya yi kaurin suna sannan yana cikin sahun gaba na manyan masu bada umurni a masana’antar ta kannywood.

Advertising

Mal aminu saira shima ya kasance jarumi kafin ya zama me bada umurni a wasu shekarun baya da suka wuce, ya taka rawar gani ba kadan ba inda ya fito a finafinai da suka hada da film din sirace na kamfanin sarauniya film production.

Amma daga baya saiya sauya akalar harkokinsa izuwa ga mai bada umurni inda yayi finafinai da suka shahara irinsu film din Mutallab, Jamila da jamilu, Ga duhu ga haske da sauransu,

Sai kuma a yanzu inda shine yake bada umurnin fitaccen shirin nan me dogon zango na Labarina wanda a yanzu haka shirin ya samu karbuwa a wajen jama’a.

Advertising

Malam Aminu saira ya bada gudumuwa ba kadan ba acikin masana’antar kannywood tin alokacin baya wanda har a yanzu yanaci gaba da bada gudumuwa.

  1. Salisu T Balarabe

Jarumi na uku shine Salisu T balarabe shima dai wannan jarumi ya jima a masana’antar ta kannywood kasancewar baiyi wasu finafinai masu yawa ba yasa ba kowa ne yasan shi ba.

Amma a yanzu yana daya daga cikin Ma’aikatan gidan talabijin ta arewa24 sannan kuma yana daya daga cikin manyan masu bada umurnin fitattun shirye shiryen nan masu dogon zango Kwana casa’in da kuma Dadin kowa.

Wanda gidan talabijin ta arewa24 take haskawa a duk ranakun maku, Salisu T balarabe ya kasance jarumi ne alokacin baya inda a yanzu shima ya sauya izuwa ga mai bada umurni.

  1. Mansoor Sadiq

Mansoor sadiq tsohon jarumin Kannywood wanda mutane da dama sun manta da fuskarsa ganin yadda ya kwashe shekaru da dama ba tare da ganin sa acikin finafinai ba, shima ya bada tasa gudumuwar ba kadan ba acikin masana’antar shirya finafinan hausa.

Mansoor yayi finafinai da dama tare manyan jarumai irin su Ali nuhu, sani danja, adam zango,da sauran su, Acikin finafinan da mansur yayi sun hada da film din Jigo, Tutar so, zakka, tururuwa, babban gari da sauran su, an samu shekaru da dama ba’a ganin jarumin acikin finafinai.

Amma daga bisani sai jarumin ya dawo cikin masana’antar ta kannywood amma shima saiya sauya al’amuran sa izuwa ga mai badaumurni da kuma shirya finafinai, shima wannan har a yanzu bai gajiya ba wajen bada gudumuwa dacigaban masana’antar ta kannywood.

  1. Hassan Giggs

Jarumi na hudu shine Hassan giggs wanda alokacin baya ya kasance mai dokar hoton ne tun kafin ya zama me bada umurni, hakan yasa ba kowa ne ya sanshi ba kasancewar aikin Nasa na bayan fage ne.

Ya fito acikin finafinai yan kalilan, daga baya shima saiya sauya harkokinsa izuwa mai ga mai bada umurni inda yayi fice a matsayin babban darakta wanda shima yana cikin layin farko na fitattun masu bada umurni a masana’antar kannywood.

Sannan kuma shine miji ga tsohuwar jarumar kannywood muhabbat abdulsalam. wacce itama a yanzu tana daya daga cikin masu shirya finafinai, Jaruman sunyi murnar zagayowar ranar auren su inda sun kwashe kimanin batabdulsalam shekaru goma sha hudu a tare.

  1. Nazir Danhajiya

Nazir dan hajiya wanda a yanzu kusan dukkan ma’abocin kallon finafinai hausa yasan shine a matsayin mai shirya finafinai, amma a alokacin baya ya kasance jarumi inda yayi finafinai da suka hada da film din Karangiya na marigayi rabilu musa ibro.

Wanda wannan film ya dauki hankalin mutane da dama kasancewar anyi shine tare da wasu fitattun jaruman kudancin nigeria wanda hakan yasa mutane suka kagu dan kallon wannan shirin wanda ba’a saba ganin irin shiba a masana’antar ta kannywood.

Amma a yanzu Naziru shima ya sauya al’amuran sa izuwa ga mai shiryawa da kuma bada umurni, sabanin fitowa da yakeyi kawai acikin finafinai.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button