Dalilin da yasa aka taba Korar Fitattun Jarumai biyu daga ciki Kannywood daga baya kuma suka dawo.
Fitatun jaruman Kannywood biyu wanda suka Bar masana’antar daga baya kuma aka dawo dasu.
Nafisat Abdullahi
Jaruma Nafisat Abdullahi daya daga cikin mayan jarumai da suka shahara itace jarumar da ta lashe kyautar gwarzuwar Jarumar Kannywood a shekara ta 2013.
Jarumar tayi Fice ne acikin film din sai wata rana na kampanin FKD production, daga nan jarumar ta kara fitowa a Finafinai da taka rawar gani irin su Ahlul kitab, toron giwa, ya daga Allah da kuma auren tagwaye.
Har a yanzu dai tauraron jarumar yana ci gaba da haskawa inda a yanzu itace jarumar da take jan ragamar fitaccen shirin nan na Labarina wanda darakta mal Aminu saira yake gabatarwa.
Sai dai jarumar ta fuskanci wata Matsala a 2013 da hukumar shirya finafinan hausa, yayin da ta shirya wani party daya sabawa ka’idojin hukumar ta Kannywood.
Wanda har hakan yayi sanadiyyar dakatar da ita daga Masana’antar na wasu shekaru, wanda hakan shine ya zama hukunci da akayi mata akan sabawa Hukumar da tayi.
KARANTA: Jaruman Kannywood da Suka sauya Akalar su Zuwa ga Masu bada Umurni (Directors)
Rahama Ibrahim Sadau
Fitacciyar Jarumar finafinan hausa Rahama Ibrahim da akafi sani da rahama sadau jarumar tana daya daga cikin manyan jaruman Kannywood, da suka samu Nasarori da yawa.
Duk da cewa jarumar bata kwashe wasu shekaru ba amma Allah ya daukaka ta fiye da sauran jarumai.
Jarumar tayi fice a film din gani ga wane a shekara ta 2013, ta kara fitowa a Finafinai da suka samu karbuwa, jarumar dai taja baya ga fitowa a cikin fina finan Hausa.
Kasancewar a yanzu tafi bada karfi a finafinan Nollywood da ake gabatar dasu a kudancin Nigeria.
Itama wannan jaruma ta fuskanci wata matsala a shekara ta 2015 inda ta fito a wata bidiyon waka tare da wani mawakin hiphop, Wanda dabi’ar data gwada a wannan bidiyo ya sabawa ka’idojin hukumar ta Kannywood.
Wanda har hakan yayi sanadiyyar korar ta daga Masana’antar ta Kannywood.Sannan a shekara ta 2020 jarumar ta kara wallafa wasu hotuna a shafinta na Instagram wanda hakan ya jawo cece kuce a tsakanin dumbin masoyanta, harma da abokan sana’arta.
Hakan yasa da dama daga cikin abokan sana’ar nata suka ringa tofa albarkacin bakin su akan bayyanar wannan hotuna, yayin da sauran jama’a keta tura sakonni na zagi harma da tsinuwa.
Daga karshe dai jaruma Rahama Sadau ta wallafa wata bidiyo a shafin nata na Instagram inda take bada hakuri akan wannan laifi data aikata da kuma nadama akan hakan bazata kara faruwa ba.
@Hausadailynews Abubuwan da kakeyi baidace ba, sannan ba Adalci bane Kuma ko Kaine ake yima abinda kake min baza kuji Dadi ba, Kana Amfani da contents Dina na Arewapackage TV Amma fisabilillahi Tsakani da Allah baka taba fadin cewa ga inda kake samun contents dinba sannan baka embedding vedio Dina, duk abinda nake fada from A to Z shi kake maimaitawa, Allah shine yasan dai dai Amma Mutane da yawa za suyi tunanin a blog dinka nake daukar text dinda nake hada vedios dina, domin duk abinda nake fada shi kake rubutawa.
Hakan baidace ba sannan ba adalci bane Kai kanka ka sani, kamata yayi karinga embedding duk vedio dinda ka dauka, idan kayi hakan meka rasa?