Advertising
Advertising
Uncategory

Fitattun mawakan Hausa Film da lokacin su ya shude a Masana’antar Kannywood.

Kaman yadda muka saba har kullum muna kawo muku abubuwa akan abin da ya shafi Masana’antar Kannywood.

Advertising

Yau mun kawo muku jerin mawakan da sukayi bacci a kannywood, ma’ana aka denajin duriyar su.

Musbahu M ahmad wanda akafi sani da musbahu sangandale sannan kuma yayane ga fitaccen mawaki Nazir sarkin waka, musbahu ya kasance fitaccen mawaki a masana’antar kannywood sannan kuma yana daga cikin mawaka da suka samu nasarori a zamanin su.

Musbahu ya tashi da sha’awar waka da harkar film tin yana yaro, amma gurin shi be cika ba saida ya hadu da fitaccen darakta Aminu Mohd sabo me kamfanin sarauniya films production.

Advertising

Inda ya bashi dama ya rera wakar shi ta farko “Allura da zare” daga nan musbahu yaci gaba da rera wakoki irin su Sangaya, dawayya, Samodara, kansakali, da dai sauransu hakan yasa tarihi bazai manta dashi ba.

KARANTA: Furodusa Abdul’amat Ya Gwan-Gwaje Bello Muhammad Bello da wasu kyaututuka.

Muhammad Ghali Yusuf wanda akafi sani ghalin money, haifafen garin zaria dake jahar kaduna, fitaccen mawakine wanda shaharar sa ta gayaye ko ina a lokacinsa.

Ya fara wakokin film a garin kano inda ya rera wakar shi ta farko a kamfanin zari films production, ghali yayi fice a wakar shi ta film din wasila.

Wanda wannan film yana daya daga cikin finafınan hausa da suka shahara a farkon shekara ta 2000, sannan wakar tana daya daga cikin abubuwanda sukasa film din ya shahara.

Rabi Mustapha shahararriyar mawakiya wacce Allah yayi mata rasuwa a shekara ta 2014, tana daya daga cikin fitattun mawaka wacce tarihi bazai manta da ita ba.

An haifeta a unguwar yakasai cikin birnin kano itace mawakiya ta farko acikin finafınan hausa ta shafe kimanin shekaru 25 tana waka a masana’antar kannywood.

Baya ga haka takan fito a matsayin jaruma ko uwa acikin finafinai, ta rera wakoki da dama da suka shahara irinsu mujadala, badali, da dai sauran su a karshe muna fatan Allah yaji kanta ya mata rahama Amin.

KARANTA: Dalilin da yasa aka taba Korar Fitattun Jarumai biyu daga ciki Kannywood daga baya kuma suka dawo.

Mahmood Nagudu fitaccen mawakin finafınan hausa wanda har a yanzu wakokin sa basu gushe a zukatan mutane ba.

Mahmud yayi wakoki da dama wanda suka shahara irin su garin so, Ajinabiyi, kalabaiye da dai sauran su, mahmud yana daya daga cikin jerin fitattun mawaka wanda tarihi bazai manta dasu ba.

Maryam A Baba wacce akafi sani da maryam sangandale fitacciyar mawakiya wacce tayi fice a wakar sangandale, wacce ta rera tare da mawaki musbahu ahmad.

Tayi wakoki da dama da bazasu kirgu ba, an shafe shekaru da dama ana jiran lokacin auren mawakiyar wacce sai 2019 Allah ya nufa aka daura auren ta.

An daura auren ne da wani masoyinta wanda shima mawaki ne mai suna Abdulrashid mohd ibrahim wanda akafi sani da abdul kafinol.

Mudassir Kasim fitaccen mawaki wanda ya kwashe kimanin shekaru 20 yana waka yana daya daga cikin shahararrun mawaka.

Sannan kuma na sahun gaba da akayi a masana’antar kannywood yayi wakoki da dama da suka shahara irin su gari ya waye, nagari sangaya, linzami da wuta da dai sauran su.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button