Furodusa Abdul’amat Ya Gwan-Gwaje Bello Muhammad Bello da wasu kyaututuka.
Shahararren Furodusa a Masana’antar fina finai ta kannywood ya yi wata gwagwabar kyautar mota zuwa ga Bello Muhammad Bello wanda akafi sani da ‘General’
Fitacciyar Jaruma masana’antar kannywood Maryam Aliyu Obaje, wadda kowa yafi sanin ta da Madam Korede ta bayyana hakan a shafin ta na Instagram, inda ta ce, Alhamdulillahi. Ina jarumi Bello Muhammed Bello murna.
KARANTA: Dalilin da yasa aka taba Korar Fitattun Jarumai biyu daga ciki Kannywood daga baya kuma suka dawo.
A ranar Juma’a data gabata ne Bello din ya sanya hoton Furodusa Abdul Amart a shafinsa na Instagram a wani rubuce-rubuce da yake yi da ya sanya wa suna ‘mai mutunci challenge, Inda zai saka mutum sannan ya fadi mutuncin da kake dashi.
Ya fara da Abdul Amart, inda ya bayyana cewa Abdul amar ya bashi mota haka kuma ya yi masa kyaututuka da dama da Canjawa yan tagwayen sa makaranta.
Shahararren Furodusa Abdul Amart dai ya sha raba motoci a Masana’antar Kannywood, baya ga sauran kyaututtuka da yake bawa jarumai iri-iri.
Mungode da ziyartar shafin mu, ku cigaba da kasancewa damu domin samu sabbin labaran kannywood.
2 Comments