An Fara Biyan Matasan Da Aka Rike wa Kudadensu: N-Power.
Za’a fara biyan Samarin da suka yi aikin N-Power a shekarun 2016 da 2018, kudadensu da Federal government ta rike su.
Tun shekarar 2020 ma’aikatar ta bada umarnin dakatar da biyan matasan albashi su mutun 14,021 sabida wusu dalilai daban daban.
A cikin matasan da aka dakatar ciki har da wanda aka gano suna karbar albashi a wasu Ma’aikatan gwamitin da Hukumomi, Sabanin ka’idar da hukuncin N-Power ta gidandaya akan banda masu aikin gwamnati.
Wannan dalili yasa Hukumar N-Power ta dakatar da biyan matasan albashin su.
Wannan bayani ya fito ne a ma’aikatar kula da ayyukan jinkai da kyautqtq rayuwa ce ta fitar da wannan sanarwa.
Bashir Nura Alkali wanda shine Sakataren Ma’aikatar ya shaida mana cewa: bayan an gama gudanar da bincike an tantance 9,066 daga cikin matasan domin biyan su kuma kowannensu za a bashi N150,000 ga duk mutum daya.
Sauran ragowar mutun 4,955 an rike nasu kudaden har zuwa lokacin da za a gama gudanar da bincike, Duk kuma wanda aka samu da aikata lefi da ake zargi zamu dauki kwakwaran maraki akansa, Inji Sakatare Bashir Nura Alkhali.