Advertising
Advertising
Labarai

Gwamnatin kano ta dakatar da nuna fina finai da ake Garkuwa da mutane.

Hukumar tace fina finai ta jihar kano ta bada sanarwar dakatar da yin fina finai masu nuna Harkar shaye shaye da kuma nuna kwacen waya ko garkuwa da mutane, wannan sanarwa ta fito daga LIB.

Advertising

Shugaban hukumar tace fina finai ta jahar kano Ismail Na’abba Afakallah ne ya sanar da wannan umarni, inda yace hakan zai dakile koyan harkar ta’addanci a jahar.

KARANTA: Jaruma Mansura Isa ta zazagi manyan kasar Nigeriya.

Kaman Yadda Rahoton Ya Fito Daga LIB

Advertising

Afakallah yace:

Daga Yau mun dena bari ana nuna fina finan da suke nuna shaye-shaye harkar garkuwa da mutane ko kwacen waya.

Ya kara da cewa:

Ba kowane yaro bane zai iya kallon abin a matsayin Film, Wani yaron a matsayin gaske zai dau abin, Daganan kuma ya je ya aikata. Dan haka dole mu dakatar kafin faruwar hakan.

Ba wannane karo na farko da gwamnatin kano ta taba yin kurin dakatar da fina finai da ake nuna shaye shaye da Garkuwa da mutane ba.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button