Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jaruman Kannywood mafi tsadar albashi a masana’antar kannywood.

Hausa Daily News ta kawo muku tarin jaruman da kuma abin da suke dauka a masana’antar ta kannywood.

Advertising

RAHAMA SADAU

Jaruma rahama sadau wacce ta shahara matuka acikin masana’antar kannywood, wannan jaruma ta bayyana cewa tin tana karamar yarinya take da sha’awar rawa da harkar film, amma bata fahimci hakan ba saida ta girma.

Ta shiga harkar film ne a 2013 kuma tayi fice a fim din Gani ga wane jaruma rahama sadau tana cikin jerin fitattun jarumai mata wanda albashinsu keda tsada a masana’antar 9.

Advertising

NAFISAT ABDULLAHI

Nafisa Abdullahi fitacciyar jaruma wacce ta lashe lambobin da yawa kamar su kyautar yar wasa mafi kyawu a kyautar City people entertainment Award a 2013.

Auren tagwaye da dai sauran su, itama wannan jaruma tana cikin jerin fitattun jarumai mata mafi tsada a masana’antar kannywood.

HADIZA GABAN

Hadiza Aliyu gabon wacce akafi sani da Hadiza gabon tana daya daga cikin jarumai masu hazaka, tazo Nigeria domin ta shiga harkar film, jajir cewa da kwazo yasa ta koyi turanci da Hausa acikin kankanin lokaci.

Ta fara harkar film a 2009 inda ta samu kyaututtuka da yawa wanda daga cikin su akwai kyautar gwarzuwar jarumar kannywood, wannan jaruma tana daga cikin jarumai mata mafi tsada a masana’antar kannywood.

MAIMUNA GOMBE

Maimuna Abubakar wacce akafi sani da Momee gombe wacce a yanzu haka tana cikin jerin fitattun jarumai wanda tauraronsu yake matukar haskawa.

Duk da kasancewar bata dade a masana’antar kannywood ba amma ta samu nasarori da dama wanda ba zasu kirgu ba, hakan yasa ta shiga cikin jerin mata mafi tsada a masana’antar kannywood.

Mungode da ziyartar shafin mu, ku cigaba da kasancewa damu domin samun abubuwan da suka shafi kannywood dama kasa baki daya.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button