Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Asiri ya tonu an Gano Jarumin kannywood din da yay wa maryam Yahaya asiri.

Maryam yahaya ta kasance fitacciyar jarumar finafinan hausa ta farko da ta ci karo da bakin tsafin da ya kusan Zama ajalinta.

Advertising

Mutane da dama a farkon lamarin sun yi tsammani kawai wata rashin lafiya ce Ubangiji ya dorawa Maryam Yahaya domin ya jarrabi imaninta kamar yadda tsarin rayuwar dan Adam take.

To sai daga bisani da likitoci su ka yi iyakokarinsu abu ya gagara sannan kuma babban abin da ya daurewa Yan uwan Maryam Yahaya kai shi ne yadda aka dauketa zuwa babban asibitin da ke da manyan kwararrun likitocin da muddin aka wuce su to sai dai a tafi kasar waje amma duk da haka sai gashi kullum ciwo sai kara tsananta ya ke yi.

Daga karshe dai abu har ya Kai ga Maryam Yahaya bata iya gane komai da kowa, hakan ya sanya danginta su ka fara fidda rai daga damuwarta.

Advertising

Sai dai kuma daga bisani bayyanar wani malami ya kawo sauki cikin lamarin ciwon Maryam Yahaya inda ya tabbatar wa da iyayenta cewa tana fama da bakin tsafin da wani abokin aikinta ya yi mata jifa da shi.

KARANTA: kalli jerin jaruman Kannywood mata 20 da baku san suna da ya’ya ba.

Bayan an mayar da Maryam Yahaya gida sai malamin ya ci gaba da bata magani tare da yi mata rukiyya da kuma karatun al-Qurani har Allah ya kawo mata sauki.

Sai malamin ya bayyana mata cewa wani abokin aikinta ne wanda ya kasance mawaki ya aikata mata wannan sammun kuma rayuwarta ya nema Allah ya tsareta.

Malamin ya bayyana sunan mawakin sai dai kuma kannywood ta nemi da a sakaya sunan nasa.

Kuci gaba da kasancewa tare damu domin kawo muku rahoto akan abinda yake faruwa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button