Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jaruman kannywood da suka Aurar da ya’yan su ga Abokan sana’ar su.

A yau muna dauke da jaruman kannywood wanda suka hada aura tayya tsakanin ya’yan su da wasu jarumai a Masana’antar.

Advertising

Rabi’u Rikadawa

Rabiu Rikadawa Dan wasan fina fınan Hausa wanda ya dade yana gudanar da wasan kwaikwayo tun kafın ya shiga cikin masana’antar kannywood, jarumin dai dan asalin jahar kaduna ne, kuma ya dade yana gabatar da wasan kwaikwayo a gidan talabijin ta NTA kaduna.

Inda suke gabatar da shirin Babangida Ramota a duk ranar asaba, akwai sauran jarumai da ake gudanar da wannan shiri tare dasu, irin su marigayi Ayuba Dahiru wanda akafi sani da tanda tare da Ladidi Tubeless, Rabiu Rikadawa yayi fice a kannywood tun a shekarar 2015.

Advertising

Duk da kasancewar yayi finafinai a baya inda ya fito acikin film din wasila wanda jarumi Ali nuhu ya jagoranta na kamfanin lerewa production.

KARANTA: Jaruman Kannywood mafi tsadar albashi a masana’antar kannywood.

Rabiu rikadawa ya aurar da diyar sa ga jarumi salisu Abdullahi wanda akafi sani da babangida an daura wannan aure a ranar juma’a 5 ga watan February acikin Shekara 2021, an daura auren jarumin da santaleliyar sahibar tasa fatima Rabiu Rikadawa.

An daura auren ranar juma’a bayan idar da sallah a kabala junction cikin jahar kaduna akan sadaki naira dubu N100,000 yan film da mawaka da dama sun halarci daurin auren wasu daga cikin sun hada da, adam zango, Aminu Saira, Alhassan Kwalle, Umar M Sharif da Sauransu.

Amaryar dai ta bayyana mahaifin nata a matsayin mutum mai kwazo da son yaga ya kyautatawa iyalinsa sannan kuma yana zama suyi hira cikin nishadi da annashuwa, tana kuma matukar kaunar yadda yake kokarin zama tare dasu duk da yanayin aikin sa mecin lokaci.

Haka zalika ta bayyana cewa babban abinda yake batama mahaifin nata rai shine; yasa mutum abu yaki yinsa alokacin da ya umar ta.

Aure dai yar gida ce akayi domin duk wanda yasan Rabiu Rikadawa to ya sanshi da babangida domin wasu da dama babangida Rikadawa suke kiransa dashi, wasu kuma sun dauka dansa ne.

Babangida dai yaron rabiu rikadawa ne na cikin indusrti kuma gashi an karfafa zumunci inda a yanzu ya zama daya daga cikin sirikin sa. Muna fatan Allah ya basu zaman lafia me daurewa Ameen.

Asama’u

Asma’u sani ta aurar da diyar ta ga fitaccen jarumin finafınan hausa jamilu ibrahim wanda akafi sani da jamilu home alone an daura wannan aure a shekara ta 2012 inda Allah ya azurtasu da haihuwar yara maza da mata.

Jarumin yayi murnar zagayowar ranar auransu tare da matar tashi wanda a yanzu sun kai kimanin shekaru tara 9 a tare muna fatan Allah ya basu zaman lafia Ameen.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button