Advertising
Advertising
Labarai

Na sha wahala matuka kafin Mahaifina ya amince na shiga gasar kyau ta Nageriya, cewar Shatu Garko

Na sha wahala matuka kafin Mahaifina ya amince na shiga gasar kyau ta Nageriya, cewar Shatu Garko

Shatu Garko wanda ta kasance Saraunitar kyau ta 44 a Nageriya, ta bayyana yadda ta sami nasarar shawo kan Mahaifin ta har ya amince ta shiga wannan gasar da tayi nasara a kai.

Advertising

Shatu Garko ita ce Mace ta farko data lashe wannan gasar tun da aka fara a shekarar 1957 kamar yadda ta shaidawa Jaridar The Punch, a lokacin da suka yi shira da ita.

Shatu Garko ta bayyana cewa: Mahaifiyata dama tana goyon bayana kuma ta na nuna min ba wani abu mai wahala bane, amma mahaifina ne baya so.

Mahaifina ya damu don gudun kada su tilasta ni in cire hijabi na ko insa kayan wanka ko kuma su mayar da ni gefe saboda rufe surar jikina da nayi. Mahaifiyata da ni mun taru muna ba shi baki sannan ya amince, da amincewarsa na yi gasar.

Advertising

Shatu Garko ta kara da cewa: ‘Yan bani na iya suka dinga caccakar ta inda su ka dinga cewa zata kai Boko Haram cikin gasar.

Bayan haka tace: Mutane sun dinga caccakar ta wasu su na cewa ta koma makaranta ta yi karatu maimakon shiga gasar.

Eh ba ‘yan arewa kadai ba har wasu daban sun caccake ni. Wasu sun dinga cewa zan bata sunan gasar. Akwai wadanda su ka dinga cewa zan kai ‘yan Boko Haram ko kuma makiyayan Fulani cikin gasar. Kawai share su nayi.

Ta kara da bayyana yadda lokacin da ta shiga gasar ba ta yi tunanin za ta ci nasara ba amma ta jajirce da kwarin guiwa har ta samu nasarar.

Garko ta lashe gasar ne a ranar Juma’a, 17 ga watan Disamba inda ta kasance mace ta farko daga Kano da ta bige mutane 17 ta ci nasarar.

An yi gasar ne a jihar Legas kuma ta samu kyautuka kamar N10m, zama a katafaren gida na shekara daya, sabuwar mota da kuma damar tallata kaya da dama.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button