Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Jaruman Kannywood da suka fi kowa yawan haihuwar yara.

Adam Abdullahi zango fitaccen jarumin finafinan hausa wanda akafi sani da prince zango wasu kuma suna kiranshi da da usher saboda gwani ne awajen taka rawa, Adam zango yana cikin jerin yan wasan hausa da sukafi kowa yawan haihuwa duk da kasancewar yayi aure aure da yawa inda ya auri mata har guda shida.

Advertising

Matarshi ta farko itace Amina wacce ya aureta a 2006, itace mahaifiyar dansa na farko me suna Aliyu wanda ake kira da haidar, bayan rabuwar su matarshi ta biyu itace Aisha wacce ya auro ta daga zaria cikin jahar kaduna.

KARANTA: Asiri ya tonu an Gano Jarumin kannywood din da yay wa maryam Yahaya asiri.

Sannan ya auro maryam daga jahar nasarawa, bayan sun rabu saiya auri jarumar kannywood Maryam AB yola wacce sukayi film din NAS tare da ita, itama auren be dade ba saiya sake auro ummukulsum daga kasar cameroon itama dai auren be dade ba saiya auro safiyya.

Advertising

Wacce itace matar shi ta shida kuma itace wacce yake tare da ita a yanzu, babu wata majiya data san dalilin da yasa yake rabuwa da matan nasa.

Acikin jerin mata shida daya aura Allah ya azurta shi da haihuwar yara shida maza hudu da mata biyu Aliyu, Khalifa, Amir, Sultan, Mubeena, da kuma Murjanatu wacce itace yar auta acikinsu.

Aliyu isah kibiya fitaccen mawaki wanda akafi sani da ali jita ya dade yana farantawa masoyansa rai musamman wakokin soyayya, biki, da sauran su, Ali jita ya kware wajen wake mata hakan yasa mata sukafi yawa cikin masoyanshi.

Ali jita ya auri matarshi me suna Nafisa a shekara 2009 yayi mata wakoki da dama har zuwa yanzu dai mawakin bai kara aure ba, inda Allah ya azurtasu da haihuwar yara biyar Usman, Aliyu, Ahmad, Zainab, da kuma Aisha wacce ita yar auta.

Hafsat ahmad idris fitacciyar jaruma sannan kuma yar kasuwa, wacce akafi sani da barauniya itama tana cikin jerin fitattun jarumai da sukafi kowa yawan haihuwa.

A kwanakin baya jarumar ta aurar da diyar ta farko me suna khadija, mutane sunyi mamakin jin labarin aure kasancewar ba kowa ne yasan tana diya data isa aure ba

Jarumar tayi aure har sau biyu inda Allah ya azurta ta da haihuwar yara guda biyar 5 mata hudu da namiji guda daya.

Sani musa danja wanda akafi sani da sani danja fitaccen jarumin finafınan hausa sannan kuma mawaki wanda ya kwashe kimanin shekaru 20 a masana’antar kannywood.

Sani danja ya auri mansura isah a 2007 wacce itama fitacciyar jarumar kannywood ce, suna daya daga cikin jaruman kannywood da suka auri junan su duk da kasancewar a yanzu sun rabu, amma sun kwashe kimanin shekaru goma 14 a tare Allah ya azurtasu da

Haihuwar yara guda hudu 4 wanda acikin su akwai Khadija, khalifa, yakubu, da kuma sudais wanda shine karami acikin su.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button