Adadin kudaden da ake biyan jaruman kwana chasa’in guda biyar.
Tabbas daya mutabe basu san yawan albashin da jaruman shirin kwana chasa’in ke dauka ba.
Sani muazu wanda akafi sani da bawa mai kada acikin shirin kwana casain fitaccen jarumi ne kuma shirya finafinai, yana daya daga cikin manyan jarumai masu gudanar da harkar film a arewaci da kuma kudancin nigeria.
Wannan jarumi dan asalin jos ne wanda ya kwashe shekaru 20 yana harkar film wannan jarumi yana daya daga cikin manyan jarumai na cikin shirin kwana casain wanda akafi biya albashi me tsoka.
Aliyu hussaini wanda akafi sani da Sahabi madugu acikin shirin kwana casain, wannan jarumi yana daya daga cikin manyan jarumai da suka kara sanya tashar Arewa24 da.
Kuma shiri mai dogon zango kwana casain ya samu karbuwa a wajen jama’a ganin yadda yake tsaida gaskiya akan aikin sa wannan shine no 2 acikin jerin manyan jarumai da akafi biya albashi me tsoka na shirin kwana casain.
Rahama miftahu wacce akafi sani da rahama MK ko kuma fulani acikin shirin kwana casain, wannan jaruma ta kwashe shekaru 7 aikin masana’antar kannywood tayi fice acikin shirin kwana casain.
KARANTA: Lilin Baba – Rigar So
Wanda ya taimaka mata kasancewar yanzu tana daya daga cikin manyan jarumai da ake nema a masana’antar kannywood wannan jaruma itace ta 3 cikin wanda akafi biya albashi me tsoka cikin shirin kwana casain.
Sahir Abdoul wanda akafi sani da Malam ali acikin shirin kwana casain, wannan jaruma duk da kasancewar be dade a masana’antar kannywood ba.
Amma yayi fice ne acikin shirin kwana casain wanda a yanxu yana daya daga cikin manyan jaruman da ake nema a masanaantar kannywood sannan yana daya daga cikin wanda akafi biya albashi.
Maryuda yusuf wacce akafi sani da salma kwana casain wannan jaruma yar asalin garin kano ce, wacce tafi fitowa acikin bidiyon waka tayi fice aciki shirin kwana casain inda har aka mata lakabi da salma kwana casain itama tana cikin jerin wanda ake biyan albashi me tsoka.