Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

jerin matana kannywood 6 da sukafi kowa daukar wanka a masana’antar

Hausa daily News tazo muku da jerin jaruman Kannywood din da sukafi kowa iya daukar wanka a masana’antar.

Advertising

(1) Jaruma ta farko itace Jaruma Fati Washa wacce asalin sunan ta shine Fatima Abdullahi tayi fice a fim din ya daga Allah.

Wannan jaruma ta kasance wacce akafi yawan magana a shekarar 2016 har zuwa shekarar 2019 saboda yawan daukar wankan ta.

Fati Wahsa

(2) Jaruma ta biyu itace jaruma Nafisa Abdullahi fitacciyar jarumar kannywood wacce yar asalin garin jos ce.

Advertising

Tayi fice ne a fim din sai wata rana na kamfanin FKD production. Jarumar tana zan hankalin mabiyanta da dama inda take wallafa zafafan hotunan ta a shafinta na instagram. Kuma jarumar ta kasance gwana a wajen daukar hoto.

Nafisat Abdullahi

(3) Jaruma ta uku itace Hadiza Gabon wacce yar asalin kasar gabon ce kuma asalin sunanta shine Hadiza Aliyu gabon.

Jarumar ta janyo cece kuce a shekarar ta 2020 inda ta wallafa zafafan hotunan ta a shafinta na instagram data dauka a kasar dubai.

Jarumar ta kasance ta uku acikin jerin matan kannywood da sukafi kowa iya daukar wanka.

Hadiza Gabon

(4) Jaruma ta hudu itace jaruma Momee Gombe duk da kasancewar jarumar bata dade a masanaantar kannywood ba. Sannan kuma tafi fitowa a bidiyon wakoki wanda tayi fice a wakar jaruma ta hamisu breaker.

Jarumar ta taka rawar gani ba kadan ba ganin yadda ta tara masoya acikin kankanin lokaci. momee gombe ta kasance jaruma ta hudu acikin jerin matan da sukafi kowa iya wanka a kannywood.

Momee gombe

(5) Jaruma ta biyar itace Bilkisu Shema wacce yar asali jahar katsina ce tayi fice a fim din tabbatacen al’amari.

Bilkisu tana yawan zan hankalin mabiyanta kasancewar yadda take daukar wanka a shafinta na instagram.

Jaruma bilkisu shema ta kasan ce ta biyar a jerin matan kannywood da suka fi kowa iya daukar wanka.

Bilkisu Shema

(6) Jaruma ta shida itace Aishatul Humaira wacce asalin sunanta shine Aisha Ahmad idris, Duk da cewa bata dade da fara fitowa a finafinai ba, amma tayi fice ne a fim din hafiz na kamfanin FKD production.

Ta kasan ce gwanar iya daukar wanka duk da cewa ta rajaa akan kayan mu na hausawa.

Mungode da ziyartar shafin mu, ku cigaba da bibiyar mu dan samun zafafan labarai.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button