Boyayen sirri da baku saniba a wajen wasu mawakan Kannywood.
Wasu daga cikin manyan mawakan kannywood kenan da suka aje tarihi a idon duniya.
(1) Nura M Inuwa wanda a yanzu ma wasu ke kiranshi da sarkin waka, ta yadda yake sarrafa harshen sa yadda yake so wannan mawaki ya taka rawar gani ba kadan ba daga shekara ta 2009 har izuwa yau.
Mawakin yayi alkawari ga masoyan sa cewa zai ringa kawo masu Albums guda biyu duk shekara.
Kadan daga cikin Albums dinshi akwai Mai zamani, rigar aro, wasika da dai sauran su.
(2) Hamisu breaker wannan mawaki ya kware matuka ta hanyar sarrafa kalaman soyayya acikin wakokin sa.
Mawakin ya jajir ce kwarai don ganin ya farantawa masoyan sa rai, inda mawakin ya aje babban tarihi a wakar sa ta jaruma.
Hakan yasa sauran kasashen africa dama duniya baki daya suka nuna mashi matukar soyayya.
(4) Umar M shareef wannan mawaki ya kasance fitaccen mawaki a masanaantar kannywood.
Umar m shareef yayi fice matuka a wakokin sa masu sanyaya zuciya kadan daga cikin wakokin sa da suka fito dashi akwai irin su rariya, mariya, hafız da dai sauran su.
Wannan mawaki ya taka rawar gani ba kadan ba ya kuma jajir ce inda yanzu haka har kasashen waje yake fita domin daukar bidiyon Album dinsa.
(5) Ado gwanja wanda asalin sunanshi shine Adam wannan mawaki ya kasance me fitowa dan daudu da kuma wasan barkwanci acikin finafınan hausa kafın ya zama mawaki.
Gwanja ya taka rawar gani ba kadan ba duk da kasan cewar mafi yawancin masoyansa mata ne Ado gwanja yayi fice ne wakokin sa guda biyu Kujerar Tsakar gida da kuma Asha rawa rawa.
Mungode da ziyartar shafin mu, ku cigaba da kasan cewa damu dan samun zafafan labarai.