Labaran Kannywood

Matsanancin halin da Maryam Booth ta shiga bayan mutuwar mahaifiyar ta.

Fitacciyar jaruma kuma shahararriya a Masana’antar kannywood wadda aka fi sani da Maryam Booth.

Maryam Booth ya ce ga marigayiya Hajiya Zainab Booth, maryam ta dade tana fitowa a fina finai tun tana karamar ta.

Maryam ta shaidawa manema labarai cewa masu shirya fina-finai (Producers) sun daina sakata a cikin fina-funan su.

Jarumar ta alakanta hakan da bayyanar bidiyon tsiraicinta a shekarun baya kamar yadda Neptune Prime ta ruwaito, Tun ina karamama kasance ina fitowa a fina-finan Kannywood, saboda mahaifiyata Hajiya Zainab Booth (Allah yaji kanta.

Ta dade a cikin masana antar, don haka bata taba daina fitowa a fina-finai haka kawai ba. Amma tunda wani matashi da ake Kira Dezeel wanda ya yi ikirarin cewa saurayina ne ya bayyana hotunan tsiraici na a kafafen sada zumunta, yanzu mutane na yi min kallon yar isaka mara tarbiyya”. In ji ta.

Jarumar wadda jaridar Daily times ta gano yanzu haka ta koma garin abuja da zama ita da dan uwanta Amude Booth tun bayan rasuwar mahaifiyar su.

Maryam tace a yanzu haka duk lokacin da mutane suka ganta suna mata kallon yar iska mara tarbiya.

Ta kara da cewa yanzu haka ba abin da take sonyi face tayi aure.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button