Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Yadda Jarumin kannywood hamza ya koma bayan an masa aiki.

Allah sarki, Rayuwa kenan hakika bazaka tabbatar da an gama halittar ka ba har sai lokacin da ka koma ga mahaliccin ka.

Advertising

Mun san duk masu bibiyar al’amuran da suka shafi Kannywood bazasu manta da wannan bawan Allah ba wato Hamza Yahaya, wanda ya taba haduwa da wani ibtila’i na yan fashi da makami a lokacin da sukai wata tafiya zuwa garin Legas daga jihar Kano.

Hamza Yahaya dai sun hadu da wannan ibtila’i ne na yan ta’adda tare da abokin tafiyar sa mai suna Ataka, inda yan ta’addan suka bude musu wuta.

Sai dai cikin hukuncin Ubangiji babu wanda ya rasa AN ran sa a wannan hari da aka kai musu, amma sai dai mummunan rauni da kowannen su ya samu, inda hucin harsashi ya wuce ta kusa da hancin hamza, dalilin da ya sa ya samu mummunan rauni akan hancin na sa.

Advertising

Inda shi kuma abokin tafiyar tasa wato Ataka ya samu rauni a gefen cikin sa, wanda a halin yanzu dai dukkan su anyi musu aiki a asibiti sun samu sauki sai dai canjin da Hamza ya samu akan fuskar sa.

To a jiya ne Hamzan ya wallafa wani hoton sa akan shafin sa na Instagram, inda yai wata magana mai taba zuciya kamar yanda zamu nuna muku yanzu.

Advertising

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button