Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Mu cikakkun zaurawa ne muna bukatar aure a shirye muke ga duk Namijin da zai aure mu, cewar Rashida Abdullahi mai sa’a

Tsohuwar jarumar masana’antar shirya fina-finan hausa ta jannywood Rashida Adamu Abdullahi wacce aka fi sanin ta da Rashida mai sa’a, ta bayyana ra’ayinta na neman mijin aure ga duk wanda yake bukatar auren ta.

Advertising

A lokacin da jarumar suka tattauna da wakilin Jaridar Damukaradiyya ta jaddada maganar da tayita neman mijin auren inda take cewa.

Jama’a sun sani nu Rashida Adamu Abdullahi mai sa’a tare da kawaye na su Hadiza Kabara da Teema Yola da Jamila Umar Nagudu, duk gabadayan mu cikakkun zaurawa ne idan akwai wanda yake son daya daga cikin ya fito mun shirya.

Sannan tace: Kuma zan tsaya tsayin daka a matsayin shugabar su don haka idan akwai mai bukatar auren ya fito mun shirya.

Advertising

Bayan wannan jawabi nata sai tace: Wasu suna ganin wannan maganar da nayi kamar da wasa nake don haka ba lallai bane a sami wanda tana mu balle ya auri daya daga cikin mu.

Amma ta bayyana cewa: Babu maganar wasa indai mutum ya shirya ya same ni duk wacce yake so a cikin mu idan an daidaita abin bazai zo da wahala ba.

Don haka Maza kada su dauka da wasa muke yi mun shirya auren ga duk wanda ya shirya zai aure mu indai da gaske yake yi.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button