Labaran Kannywood

Mata biyu sun ishe mu darasi a Kannywood inji Darakta sunusi oska442.

Babban mai bada umarni a masana’antar Kannywood Sunusi Oscar 442 ya cillo wata magana akan shafin sa Instagram wadda ta zama abar cece kuce a tsakanin mutane.

Hakika abubuwa da dama sun faru a cikin masana’antar ta Kannywood, wadanda suka zama izina da jan hankali ga wadanda suke da fahimta da kuma cikakken hankali.

A cikin masana’antar Kannywood anyi jarumai da dama da sukai tashe suka shahara, wadanda a yanzu haka wasu sun mutu sun koma ga Allah wasu kuma suna nan a raye amma sunaji suna gani harkar tafi karfin su.

Shiyasa duk wanda fahimci rayuwa ba zai taba yin girman kai da jiji da kai ba, domin kuwa duk tashen da yake yi wata rana ko yana so ko baya so dole ya hakura ya bar wa masu tasowa.

A baya a cikin masana’antar Kannywood anyi mashahuran jarumai kamar su Balaraba Muhammad, Amina Garba, Ahmad S Nuhu Hauwa Ali Dodo wato Biba Problem da dai sauran su wadanda dukkan su sun bar duniya sun koma ga Allah tamkar ba’ayi su ba.

Sannan kuma akwai jarumai irin su Fatima Muhammad, Fati Baffa Fage Ummi Zizi da sauran su, wadanda dukkannin su suna nan a raye amma
basa cikin harkar ta fina-finai.

To a wannan zamanin ma dai akwai wasu jarumai da rayuwar su ya kamata ta zama darasi da izini ga masu hankali, kamar yanda Darakta Sunusi Oscar 442 wallafa akan shafin sa na Instagram.

Daraktan dai yayi wannan magana ne irin wadda Malam Bahaushe yake cewa magana mai kurman baki, domin kuwa bai bayyana su wanene wadannan mata guda biyu ba.

To da fatan dai Allah Ya kyauta ya kuma yi mana mai kyau a duniya da lahira Ameen. Kuci gaba da kasancewa da tashar Kundin Shahara. Mun gode.

9 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button