Daga malamar makaranta izuwa fitacciyar jarumar Kannywood: Hadiza Gabon.
Hadiza Gaban daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood da ake ji dasu, An haifi jarumar a kasar Gaban a shekarar alaf 1989.
Jarumar ta kammala karatun ta na primary da secondary a cikin kasar ta Gabao tayi fice a masana’antar ta kannywood a shekara ta 2009.
Cikin jerin fina finai da jarumar tayi sun hada da Yar Maye, Fataken Dare, Artabu, Basaja da kuma Idon kauye, sanan jarumar tana daya daga cikin matan da suke fitowa a Nollywood inda a yanzu jarumar ta fito a Film dina LAGOS REAL fake life,
A shekarar 2019 jarumar ta kirkiri gidauniyar HGaban Foundation, wannan gidauniya tana temakawa marasa lafiya yan makaranta da gajiyayyu.
Jarumar ta sami kyaututuka da dama da suka hada da gwarzuwar jarumar Kannywood a shekara 2013, Sanan ta sake samun kautar jaruma mafi kyau a shekarar 2014.
bayan shigowar ta Masana’antar Kannywood ta kasance malamar makaranta da take koyar wa da yaran Faran Faransanci.
One Comment