Asirin wata matashiya ya tonu bayan an kamata da yar mutane.
Asirin wata matashiya yar kimanin shekara goma sha 9 ya tonu bayan ganin ta da akai da wata yar makotan su a bayan gari zasu gudu tare.
Budirwar mai suna Saddika da kuma Salma yan garin katsina karamar hukumar bindawa ta dauki yar makotar zata shiga yawon duniya da ita.
Yan bijilanti dake yanki sunyi nasarar kama yan matan biyu cikin dare a gefen wata Unguwa suna shirin bazama su shiga yawon duniya. nan dana yan bijilanti suka mikasu zuwa hukumar yan Sanda dake yanki,
Da kakakin yan sandar jihar yake zantawa da manema labarai, ya ce yan matan biyu sun shirya guduwa daga gida ne saka makon za’a aura musu mazajen da basu suke so ba.
Ya kuma ce an kira iyayen yan matan guda biyu domin aji ta bakin su. inda mahaifiya salma tace eh aure ake shirin yimata da dan uwanta suka nemeta suka rasa.
Mahaifiyar Saddika kuwa cewa tayi sun gaji da yawan ta zubar ne da yarinyar take hakan yasa suka shiya auren ta ba tare da ta saniba sai da abin ya matso.
Wannan bashi ne karo na farko da iyaye suke tilastawa yaransu wajen auren mazajen da basu suke soba,