IZZAR SO EPISODE 63 ORIGINAL.
Saban shirin Film din izzar so episode 63 original, tabbas yan kallo na zuba idon ganin mezai faru idan dan matawalle ya bayyana.
Haka kuma masu kallon wannan film mai dogon zango suna ta aiko da sako akan cewar Film din yakusa karewa,
Yan kallo sunce matukar aka ga dan matawalle cikin wadannan episode daga na 63 zuwa 70 to shirin Film din IZZAR SO ya kare, wannan magana da yan kallo suke yi yasa mashiryin film din Jarumi Lawan Ahmad ya ce, Bayyanar dan matawalle shine ma kamar farkon shirin.
Lawan Ahmad ya kara da cewa shirin Film din izzar so ba irin sauran fina finai masu dogon zango ba ne da kuka saba gani, IZZAR SO Film ne da aka tsaya aka fidda basira wajen rubuta shi.
Mashiryan shirin ya kara da cewa suna iya koksrin su wajen sunga sun farantawa masu kallon wannan shiri rai, saboda duk mai kallon Film dinka yana da muhimmanci a gareka.
A karshe lawan Ahmad yaja kunnan
masu daukar masa finna finai suna dorawa a channel dinsu dakuna yarn Download.
Mungode da ziyartar shafin mu, kuci gaba da kasancewa damu domin samun zafafan labarai.