Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Da Dumi-Dum: Hadiza Gabon ta sa an kame Auwal Isa west kan zagin da yayi mata.

Da yammaci muke samun wani labari daga shafin Instagram na Maufeeda Rasheed a dandalin Instgaram kan hatsaniyar da ke tsakanin Auwal Isa west da Hadiza Gabon inda ta bayyana tuni jarumar tasa aka kame jarumin da yayi mata zagin tsamar nama wato Auwal Isa West.

Advertising

kamar yadda wasunku suka sani Hadiza ta yi wasu rubuce rubuce da maganganu kan jaruman Kannywood da cewar sun yi shishigi wajen shigewa jarumin big brother white money, suna hotuna da shi a cewar ta da nasu ne bazasu yi musu haka ba.

Hadiza ta kara da cewa ko a story jaruman big brother din basu saka su ba balle suyi musu repost balle asan suna yi, wanda wannan magana wasu suka dauke ta a matsayin rashin kunya ga nagaba kasancewar gar da manyan jiga jigan masana’anta a cikin wayanda suka halacci taron da aka shirya irin su Baba karami, Ali Nuhu, Adam A Zango, Abba Elmustapha da sauran su.

Hakan ya sa producer Alhaji sheshe da Auwal west suka yiwa jarumar raddi sai dai shi Auwal west a nasa raddin ya kama suna Hadiza ya kuma rufe raddin nasa da zagi na tsamar nama ga wayanda yace yaran da suke wa manya rashin kunya a social media.

Advertising

Sai da kowa ya dauka magana ta wuce ashe Hadiza bata kasa ne tana birnin cairo aiko take ta dau haramar dawowa sai gata a jiya ta dira a garin kano, kamar yadda Mufeeda Rasheed ta bayyana tun Karfe biyu ranar tasa aka nemo mata shi aka kuma tsare a hannun jami’an tsaro.

Yanzu haka maganar da ake West yana hannun hukuma yayin da ita kuma Hadiza ta kashe wayar ta kiran duniya ba’a samun ta balle a bata hakuri ta sa a sake shi.

ku kasance damu dan jin yadda wannan turka turka zata kaya.

Advertising

One Comment

  1. Nidaii shawarata Dan Allah Yan kannywood kudaina fada Dan Allah bashida amfani kuda kuke fadakarwa Amma Kuma kuzo Kuna fada

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button